Babu rashin jituwa tsakanin darikar Angalika da gwamna El-Rufa’I – Liman Ali Buba Lamido

0

Babban limamin darikan Agilika na jihar Kaduna Ali Buba Lamido ya bayyana cewa babu wani rashin jituwa tsakanin mabiya darikar da gwammnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.

Lamido ya fadi haka ne a ziyarar da manyan limaman darikar na yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya suka kai wa gwamna El-Rufai a garin Kaduna.

Ya ce sun zo ne domin sun mika godiyar su ga gwamna El-Rufa’I kan dakatar da rusa cocin Angalika dake Sabon- Garin Zariya wato ‘St George’s Cathedral’.

Idan ba a manta ba gwamna El-Rufai ya umarci da a rusa cocin Angalika dake Sabon-Garin Zariya domin gyara da gwamnati za ta yi. Sai dai jim kadan bayan wannan sanarwa sai kuma gwamnati ta hanye wannan shiri.

A wancan lokacin gwamnati ta ce ta yi haka ne a dalilin kiraye-kiraye da aka rika yi mata na mahimmancin wannan ginin coci.

An ce wannan Coci ya shekara sama da 100 da gina shi wanda a dalilin haka ya sa ba wai coci ba kawai ya zama wajen tarihi a wannan gari.

Gwamna El-Rufai ya saurari wannan kuka da kunnen basira kuma ya janye wannan shawara na rusa wannan Coci.

Sai dai bayan haka kuma, sai wasu suka rika fitowa suna sukar gwamnati ta hanyar yin rubuce-rubuce na batanci ga gwamnan.

Lamido ya ce lallai ba da yawun su bane ake yada wadannan maganganu sannan kuma ya kara da cewa za su bi diddigin wannan abu domin cafke wadanda suke haka don hukunta su.

Lamido ya yaba wa El-Rufai bisa ayyukan ci gaba da yake yi a jihar gabadaya da sauraren su da ya yi.

A nashi jawabin Gwamna El-Rufai ya shaida wa tawagar limaman cewa rusa wannan coci da gwamnati ta yi yunkurin yi ba ta yi bane don ta tozarta wani addini ko kuma wani jinsi na mutane, ta yi ne da kyakkyawar niyya domin gyara jihar.

Gwamnan ya kara da cewa wannan aiki da gwamnati za ta yi zai shafi gidaje sama da gidaje 40 a Sabon-Gari sannan gwamnati ta ware kudade domin biyan mutane diyyar abinda za su rasa.

El-Rufa’I ya yi kira ga limanan da su rika ja wa mutane kunne, da kuma cafke duk masu amfani da addini suna ruruta tashin hankali a jihar. Ya ce gwamnati a shirye ta ke domin mara musu baya akan haka.

Share.

game da Author