Arzikin fetur bai iya magance matsalolin Najeriya – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Najeriya na da dimbin arzikin danyen man fetur, amma kuma matsaloli sun sha kan kasar, ta yadda arzikin ba zai iya magance su ba.

Buhari ya yi wannan bayani ne jiya Alhamis a Fadar Shugaban Kasa, a lokacin da Jakadan kasar Cuba a Najeriya, Carlos Trejo Sosa, ya je yi masa bankwana.

Sosa ya bar Najeriya ne bayan ya shafe shekaru biyar ya na wakilcin kasar Cuba a matsayin jakadan ta.

Buhari ya shaida wa jakadan cewa ya gamsu matuka da irin kawance da zumuncin da aka kulla tsakanin Cuba da Najeriya, musamman a fannin kiwon lafiya da kuma inganta ilmi da sauran su.

“ Mu na da tazgaro a fannonin gina ayyukan inganta al’umma, ilmi, kiwon lafiya da sauran wasu fannoni. Amma a ko da yaushe Cuba kan kawo mana dauki.

“Abin da mu ke samu a fannin danyen man fetur ba su isa a gudanar da dukkan ayyukan da kasar nan ke bukata ba. Sai mu ke marhabi da duk irin daukin da mu ke samu, kamar irin wanda kasar Cuba ke kawo mana a duk lokacin da hakan ta taso.

Shugaba Buhari ya ce ko lokacin da ya yi mulkin soja da kuma yanzu duk ya rika hada guiwa da Cuba domin kawo ci gaba a kasar nan.

Shi kuwa Jakada Sosa, cewa ya yi shekaru biyar da ya shafe har da kwanaki tara duk a Najeriya, ya amfana sosai da irin so da kaunar da aka nuna masa. Ya na kuma mai ci gaba da cewa, ba zai taba mantawa da Najeriya ba.

A wani taron kuma da Buhari ya yi wani jawabi, ya bayyana cewa ba a samun yanayin da masu zuba jari za su shigo, muddin matsalar harmagazar siyasa ta yi katutu a cikin zukatan al’umma.

A nan sai Buhari ya ce gwamnatin tarayya za ta yi dukkan abin da ya wajaba domin tabbatar da cewa ta kare muradin masu zuba jari a kasar nan.

Jiya Alhamis ne Buhari ya yi wannan jawabi lokacin da ya karbi bakuncin ziyarar da Shugaban Total Worldwide, Patrick Pouyanne ya kai masa ziyara.

“ Dangantaka tsakanin kamfanin Total da Najeriya dadaddiya ce, kowa na cin moriyar kowa. Don haka mu cigaba darike juna da amana, gaskiya tare kuma da yin ayyuka tare.

Pouyanne ya shaida wa Buhari cewa, baya ga aikin hako fetur da gas, Total zai iya gudanar da ayyukan samar da hasken lantarki na sola a nan Najeriya.

Share.

game da Author