Kotun dake sauraren karar da dan majalisa mai wakiltar Madobia jihar Kano Ismaila Kabir ya shigar ya inda ya saka aka tsare wani dalibin jami’ar Kano mai suna Yahuza Tijjani ta sake shi a safiyar Alhamis.
Dan majalisa ya rika gadarar cewa shi mai Kudi ne sannan babu wani da ya isa ya tilastashi shi ya saki wannan dalibi a lokacin da ya ke tsare.
Dan majalisa Ismaila ya fadi cewa saboda karfin kudi da iko da yake da shi hatta babban jojin jihar ya mara masa baya da a ci gaba da tsare wannan dalibi.
” Duk wani da ake tunanin wani babu wanda bai kira ni ba irin su Abdullahi Abass…, Domin akan wannan abun saida cif joji ya kira ni mun yi zama da Cif Joji akan wannan ya kuma kira Alkali ya bashi Umarnin ya ci gaba da daure shi.
” Duk Madobi indan ana batun ga wane shegen kansa ne, wanda a baya zai iya yin duk abin da yaga dama kowa dai ya san haka yake amma wallahi tallahi babu mutum da zai yi mun haka ya ce zai ci lafiya.Wallahi da daga kaina ba zai kara ba.
Alkalin kotun ya yanke hukuncin a saki Yahuza sannan wai za aci gaba da shari’ar ranar 10 ga watan Disemba.