An rantsar da shugabannin kananan hukumomi 12 na jihar Kebbi

0

A ranar Litini ne gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya rantsar da ciyamomin kananan hukumomi 12 na jihar.

Taron rantsar da shugabannin kananan hukumomin ya gudana ne a Birnin Kebbi. A jawabin sa gwamna Bagudu ya hori ciyamomin da suyi shugabanci cikin aminci, adalci ba tare da wariya ba.

Ya kuma yi kira garesu da su kirkiro hanyoyin da za su sama wa kananan hukumomin su kudaden shiga, sannan da samar da tsaro.

Bagudu ya yabawa kokarin da hukumar zabe ta jihar (KESIEC), jami’an tsaro, masu sa ido a zabe da ‘yan jarida kan gudunmawar da suka bada a lokacin zaben.

Daga nan a madadin ciyamomin Shehu Marshall shugaban karamar hukumar Jega ya gode wa gwamna Bagudu sannan ya ce za su maida hankali wajen ganin sun inganta rayukan mutanen kananan hukumomin su.

Share.

game da Author