Jami’ar Jihar Akwa Ibom ta bayyana korar malamai 8 da aka samu da neman yin lalata da dalibai mata su na ba su makin jarabawa.
Sannan kuma an kama su da laifin zarbar kudade a hannun dalibai ta wasu manufofi da hanyoyi daban-daban.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Ibanga ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke magana a wani taron manema labarai da ya shirya a Ikot Akpaden, cikin Karamar Hukumar Enin, a jiya Talata.
Ibanga ya ce wadanda aka korar sun rika matsa wa dalibai mata neman yin lalata da su a kakar karatu ta 2015 da 2016 da kuma ta 2018 da 2019.
“Daga yau mun soke yarjejeniyar dauka aiki da muka yi wa wadannan malamai su takwas, saboda rashin kare mutuncin su da suke yi ga dalibai mata da kuma karbar kudade a hannun dalibai.
“A zaman yanzu haka akwai wani bunsurun malami na nan ya yi bakam ya lamfale. Amma a mu fallasa shi, domin ba za mu taba bari ya ci bulus ba.
“Wasu shari’un sun a kotu. Na rantse ba zan taba bari wasu lalatattu su bata sunan wannan jami’a ba. Za mu kara tsarkake ta sosai.” Haka Ibanga ya kara jaddadawa.
Ya ce jami’ar na bakin kokarin ta wajen ganin ta wanzar da kima da mutuncin ta a idon dalibai, malamai da kowa.
Ya ce kafin jami’ar ta dauki wannan hukuncin kora, sai da ta kafa kwakwaran kwamiti, kuma ta tabbatar tare da gamsuwa da cewa dukkan wadanda ake zargin sun aikata laifukan da ake argin sun aikata.
A wannan shekara dai guguwar fallasa yadda malaman jami’a ke lalata da dalibai mata domin ciyar da su jarabawa ta mamaye jami’o’in kasar nan.
An kori malamai da dama kuma an fallasa da dama daga cikin su a jami’o’in kasar nan.
Discussion about this post