Babbar Kwalejin Fasaha ta Ozoro da ke cikin Jihar Delta, ta haramta wa daliban kwalejin saka hular nan mai ciko, da aka fi sani da hana-sallah, a cikin makarantar.
Shugaban kwalejin, Job Akpodiete ne ya bayar da wannan umarnin, a karshen makon da ya wuce, bayan da aka kone sama da hulunan hana-sallah 5,000 da aka kwace daga hannun daliban kwalejin.
Akpodiete, wanda Shugaban Kula da Harkokin Dalibai, Thomas Ojuye ya wakilta, ya ce an yi wannan umarni ne saboda a hana yawaitar shigar-banza da suturar marar mutunci a cikin kwalejin da ya ce dalibai ke yi.
“Hukumar wannan kwaleji ta fito da shawara ga dalibai cewa su rika yin shigar mutunci ba shigar fitsara ba. Su rika yin shiga wadda makarantu da sauran al’umma suka gamsu da ita.
“Biyo bayan dokar da hukumar wannan kwaleji ta kafa, daga yau an hana saka duk wata hula mai ciko a cikin wannan makaranta.” Haka ya furta.
Sannan kuma nan take shugaban kwalejin ya bai wa jami’an da ke tsaron makarantar iznin duk hular da suka kwace daga kan wani kangararren dalibi, to kone ta nan take.
Ya kwalejin ta Ozoro ta shafe shekaru da dama ba a ji tashin-tashinar rikici ko bullar kungiyoyin asiri ba.
Daga nan sai ya danganta wannan nasara ya ce kwalejin ta samu ga hobbasa da jajircewar da hukumar makarantar ta yi wajen daukar tsauraran matakan gudanar da al’amurran kwalejin.
Shi ma Shugaban Jami’an Tsaron Kwalejin Fasaha ta Ozoro, Simeon Eduke, ya bayyana kwalejin a matsayin daya daga cikin kwalejojin fasaha mafi zaman lafiya a kasar nan.
Ya ci kwacewa, hana sawa da kone hular hana-sallah da ake yi a kwalejin, zai zama wani kakkausan gargadi ga sabbin dalibai masu shiga kwalejin.