An gano yaron da aka sace a cikin 2014 a Kano a jihar Anambra –’Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sanda ta bada sanarwar ceto wani karamin yaro mai shekaru 11 da haihuwa, mai suna Muhammed Ya’u, wanda aka sace a Kano tun cikin 2014, aka arce da shi Anacha.

Wannan sanarwa ta cikin wani bayani da Kakakin Yada Labarai na ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna ya sa wa hannu kuma ya raba wa manema labarai.
Haruna ya ce wasu Inyamurai ne miji da mata, Paul Onwe da matar sa mai suna Mercy Paul suka sace yaron tun cikin 2014 a Kwanar PRP, A Kano.

Sun sayar da shi kudi hannu ga wani Inyamirin mai suna Ecere Ogbodo a kan kudi naira 200,000.

“A kokarin da jami’an mu ke ci gaba da yi domin gano sauran yaran da aka sace daga Kano ana kaiwa wani sashen kasar nan, an gano wani yaro da aka sace tun cikin 2014, a Kwanar PRP, aka saida shi a garin Anacha.

“Jami’an Operatiom Puff Adder, masu dakile satar yara da garkuwa da mutane ne suka gano su.

Haruna ya ce an sake wa yaron suna zuwa Chinedu Ogbodo. Shi Ogbodo dai shi ne aka saida wa yaron kan kudi naira 200,000.

Ya ce a yanzu haka ana ci gaba da binciken wadanda ake zargin su uku. Kuma ana ci gaba da kokarin ceto sauran yaran da aka yi ikirarin an sace a Kano.

Ya kuma gode wa jama’a dangane da irin gudummawar da suke bayarwa wajen kokarin ceto sauran yaran.

Wannan ne karo na uku da aka gano yaran da ake sacewa daga Kano ana saidawa a jihohin Inyamurai.

Yaran farko da aka fara ganowa su 9 ne. Daga baya kuma an gano wasu yara biyu da aka sace daga Jihar Gombe, sai kuma wasu yaran da aka sata daga Jihar Kebbi.

Share.

game da Author