Hukumar Babban Birnin Tarayya, Abuja ta bayyana cewa ta tirsasa wa masu baburan A Daidaita Sahu da aka fi sani da Keke NAPEP ficewa daga Abuja.
Kakakin Yada Labarai na Ministan Babban Birnin Tarayya, Anthony Ogunleye ne ya bayyana haka a yau Litinin, a cikin wata sanarwa.
Ya ce an kafa kwamitin jami’an tsaro daga fannonin tsaro daban-daban, wadanda aka dora wa alhakin fatattakar masu baburan Keke NAPEP daga Abuja.
Kimanin makonni uku kenan da aka fara hana su zirga-zirgar daukar fasinjoji a cikin Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Kafin a yi wannan fatattakar dai, masu Keke NAPEP na dauko fasinjoji da Mahadar Titin da ke daidai kamfanin Dantata and Sawoe a Garki, su bi ta Kasuwar Garki, su zarce har Area I, Area 2, Area 3 da UTC da kuma Area 10.
Akwai sauran unguwanni da dama da aka amince masu Keke NAPEP su yi aiki, musamman katafariyar unguwar nan, Gwarimpa da sauran su.
Sai dai kuma tun bayan da aka fara korar su, masu Keke NAPEP sun kaurace wa birnin Abuja.
Wakilin mu a ranar Larabar da ta gabata ya ga yadda masu baburan Keke NAPEP ke tururuwar kaura daga Abuja zuwa Arewa.
Wadannan matasa, wadanda kusan kashi 99 nisa 100 duk ‘yan Arewa ne, tuni suka fara komawa Kaduna da Kano da Zariya da Funtuwa da sauran manyan garuruwan Arewa.
Sai kuma wakilin mu ya yi ta bakin da dama daga cikin su, wadanda suka rika nuna rashin jin dadin wannan kora da aka yi musu.
“Wannan wane irin rashin adadlci ne? An san za a kore mu kuma aka nemi kuri’un mu a lokacin zabe?
“Wace irin gudummawa ke ba mu bai wa gwamnatin Buhari da APC ba? Wasun mu da dama kauyukan su suka rika tafiya domin kawai su yi zabe, don mu kayar da PDP.
“Gaskiya ni dai da na san za su kore mu, to ba zan zabi APC ba. Domin babu irin zagin da ba a yi wa gwamnatin APC, ana ce ma ta gwamnatin mayaudara, amma mu na kare ta. To a yau dai ta tabbata cewa abin na su akwai yaudara.”
Wani mai suna Kabiru ne ya rika wannan bambamin, a lokacin da wakilinmu ya zanta da shi, a daidai Kasuwar Garki, kan hanyar sa ta zuwa kauyen Apo daga can ya zarce ta Galadimawa Junction, ya kewaya ta Area I.
Wani mai suna Salisu da ya ce shi ma dan APC, ne, amma yanzu yay age hoton Buhari daga Keke NAPEP din sa, cewa ya yi, “ni abin da ma ya fi ba ni haushi, duk matasan Arewa ne aka kora. Yanzu haka ni kunyar komawa Kano na ke yi, saboda ‘yan adawa dariya za su rika yi min.”
Sai dai kuma sanarwar ta amince su rika yin haya garuruwan da ke nesa da Abuja, kamar Nyanya, Kurudu, Orozo, Karshi, Bwari, Kubwa, Lugbe, Gwagwalada, Kwali, Abaji da kuma cikin manyan rukunin gidaje, wato ‘estates’.
An Ki Cin Biri An Ci Kare
Sai dai kuma sanadiyyar korar masu Keke NAPEP daga Abuja, masu tsoffin motocin taxi da ake kyamar shiga a Abuja, a yanzu kuma su ne suka cika titinan da a da masu Keke NAPEP ke bi.
Yawancin irin wadannan motocin, dauki-ajiye suke, yi, abin da a Abuja ake cewa along, ana biyan su naira 100 kowane fasinja.
Da yake aka sarin motocin duk tsoffi ne, a yanzu haka wasu manyan titinan Abuja cunkus suke da irin wadannan motocin, wadanda idan wasu suka taso, za ka yi tunanin daga bola aka kwaso su.
Sannan kuma wasu dandazon ‘yan kwaya masu kamashon lodi daga wasu wurare, duk a yanzu sun shigo Abuja, da sunan yi wa masu motocin lodi.
A da kuwa wadannan ‘yan kwaya sun fi yin zazu da bulkarar su can a garuruwan da ke wajen Abuja.
Discussion about this post