An fara taron Mayu da Matsafa na Kwana biyu a Jihar Enugu

0

Duk da nuna kiyayya karara da aka rika yi wa wasu mabiya kungiyar Mayu da Matsafa a jihar Enugu a kokarin shirya taron ibada ta kungiyar, daga karshe dai burin su ya cika domin sun gudanar da wannan taro na kungiyar da yayi kama da taron Ibada na su.

Mabiya kungiyar Mayun sun yi wannan taro na su ne a babban dakin taro da ke jami’ar Najeriya dake Nsuka, Jihar Enugu.

Kafin a bari su shirya wannan taro na Ibada, kungiyoyin kiristoci na jihar musamman mabiya darikar Katolika sun rika yin suka akai suna yin tir da wannan kungiya sannan kuma da neman a hana su yin wannan taro.

PREMIUM TIMES ta tattauna da wani dan jarida da ya halarci taron mai suna Patrick Egwu.

A hira da aka yi da shi wannan dan Jarida ya ce tabbas ya halarci wannan taro ne domin ya gani wa kansa tabbacin ko da gaske ne akwai irin wannan kungiya sannan kuma har ta na da mabiya kamar yadda ake tallatawa?

Ya ce bayan mabiya sun halarta sai aka fara addu’o’i sannan da amshi daga mabiya. Mawaka ma sun rera wakoki na yabo kafin nan aka fara jawabai.

Egwu yace babbancin da ya gani shine a wajen jawabin manyan baki.

“Duk mai jawabin da ya yi magana a taron ya gabatar da jawabinsa ne akan Tsafi da Maita.

Ya ce tun da aka fara taron babu tashin hankali da aka samu daga bangaren mutanen da suke adawa da taron. Sannan daga wajen harbar dakin taron an rika siyar da takardu da kasidu da ke kunshe da yadda ayyukan maita da tsafi suke domin mabiya su rika karantawa.

” Duk da suka da aka rika yi wa wannan kungiya da taro, kafin kace wani abu, mutane sun cika fam a wannan dakin taro. Babban dalilin da ya sa aka shirya wannan taro kamar yadda na gani shine domin a wayar wa mutane kai game da wannan kungiya ta Mayu da rashin illar ta.

Bayan haka Mr Egwu ya ci gaba da cewa ba tun yanzu ba yake ta son sanin ko menene ya hada maita da addinin kirista domin sau da dama zaka ga mutumin da ke ikirarin wai shi kirista ne ya tashi cikin dare ya kunna wuta ya na rokon wai Allah ya kashe makiyinsa. Duk ire-iren haka ai ba daidai bane shima idan aka bi diddigi ayyukan maita ne.

” Abu daya da nake ganin ba a yi daidai ba wajen kushe wannan kungiya shine yadda ake nuna musu kiyayya. A kasashen Turai sai kaga ana ire-iren wadannan abubuwa amma muna tsalle muna yaba musu muna jin dadi wai suna burge mu amma namu sai kaga ana binshi da muggan kalamai da suka.”

Share.

game da Author