An cafke wasu dattawa biyu da suka yi lalata da wata ‘yar shekara 11 a Kebbi

0

Shugaban kungiyar ‘Kebbi Concerned Citizens (KCC)’ Ibrahim Muhammed ya bayyana cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta cafke wasu dattawa biyu masu shekaru 70 da 50 da laifin yi wa ‘yar shekara 11 fyade.

Muhammed yace wadannan mutane sun aikata haka ne ranar 31 ga watan Oktoba a karamar hukumar Gwandu.

Ya ce bayanai sun nuna cewa wadannan mutane sun rika rudin wannan yarinya ne har suka kai wani wuri suka danne ta.

“ Mun samu tabbacin an yi wa wannan yarinya fyade daga gwajin da likitoci suka yi sannan muna kuma da shaidun mutanen da suka tabbatar hakan ya faru.

Ya yi kira ga dukan kungiyoyi, iyaye da sauran mutane da su mike kai tsaye wajen yin yaki da aikata wanna mummunar aiki.

Bayan haka jami’in hulda da Jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nafi’u yace wadannan mutane sun tabbatar da aikata wannan laifi sannan suna nan tsare a ofishinsu.

Ya ce bashi da abin da zai iya cewa sai an kammala bincike akai.

Idan ba a manta ba a watan Oktoba ne hukumar kare hakkin dan adam ta kasa (NHRC) ta koka kan yadda yi wa mata fyade ke neman zama ruwan dare a wasu jihohin rewacin Najeriya.

Kodinatan hukumar Mohammed Ayuba ya ce yawa-yawan yi wa mata fyade a jihar na da nasaba ne da rashin kiyaye dokoki da mutunta al’umma,rashin bin iyaye da rashin samun tarbiya nagari.

Share.

game da Author