Amosun ya shigo da bindigogi 1,000 da harsasai ba tare da izini ba – Gwamnati

0

Gwamnatin Najieriya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa tsohon Gwamnan Jihar Ogun Ibikunle Amosun bai tsaya karbar izni ba ya yi sumogal din muggan makamai cikin Najeriya.

A cikin wata wasika da Darakta Janar na Kasafin Kudin Gwamnatin Tarayya, Ben Akabueze ya aiko wa PREMIUM TIMES kwanan nan, y ace abin da Amosun ya nemi iznin sayo su ne motocin daukar jami’an ‘yan sanda 13 tun a cikin 2012.

Amosun ya yi gwamnan jihar Ogun daga 2011 zuwa 2019. Ya tsaya takarar sanata a APC a lokacin da ya ke daf da kammala wa’adin san a gwamna, kuma ya yi nasara.

PREMIUM TIMES ta fallasa Amosun a cikin watan Yuni, inda ta fayyace yadda ya damka wa jami’an tsaro bindigogi 1,000 da harsasai milyan biyu da rigunan sulken hana harsashi huda mutum, ta tare da gabatar da shaidun cewa a bisa ka’ida ya shigo da makaman ba.

Jami’an tsaron da suka gulmata wa PREMIUM TIMES labarin yadda ya mika makaman, sun kara tabbatar da cewa akwai damuwa sosai idan aka bi diddigin yadda Amosun ya mallaki makaman masu tarin yawa, wadanda ya mika wa jami’an ‘yan sanda kwana daya kafin cikar wa’adin mulkin sa.

Wasu majiyoyin kuma sun kara cewa jami’an tsaro sun rika sa-ido sosai a kan Amosun a lokacin da zaben 2019 ya gabato, don kada ya zille ya yi amfani da wadannan muggan makamai wajen damka su ga ‘yan dabar siyasa.

Har yau kuma jami’an tsaro sun cika da mamakin yadda aka yi har Amosun a lokacin da ya ke gwamna ya iya yin sumogal din wadannan makamai masu yawa.

Sannan kuma a na ta tunanin abin da ya yi niyyar yi da su da kuma hakikanin yawan su.

Wato su na tunanin watakila ma makaman da ya shigo da su din sun zarce yawan wadanda ya damka wa jami’an tsaro a ranar jajibirin da zai sauka daga mulki.

Da farko lokacinn da PREMIUM TIMES ta fara buga labarin, Amosun ya shiga shafin sa na Twitter ya karyata.

Daga baya kuma ya ce ya samu satifiket daga Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro, ya shigo da motocin daukar ‘yan sanda 13, bindigogi samfurin AK47 guda 1,000 da kuma harsasai milyan 2 a cikin 2012.

Amosun ya ce ya sayo makaman ne da nufin bai wa ‘yan sandan jihar sa gudummawar dakile aikata miyagun laifuka a jihar.

Ba wanda ya ba Amosun Izinin Shigo da Makamai

A wasikar da Akabueze ya rubuto wa PREMIUM TIMES, ya bayyana cewa:

“Bayan nayi nazarin tambayoyin da ku ka bukaci amsa, to ina mai sanar da ku gaskiyar lamari cewa Sanata Ibekunle Amosun, tsohon gwamnan jihar Ogun ya nemi iznin shigo da motocin daukar ‘yan sanda guda 12.

“Ya aiko da wannan takardar neman izni a ranar 10 Ga Afrilu, 2012, kamar yadda wasikar sa mai lamba BO/R.10260/S.4/T.4/22 ta tabbatar.

Wadannan motoci kamar yadda wasikar ta nuna, za a yi amfani da su ne wajen sintiri na hadin-guiwa tsakanin sojoji da ‘yan sanda a jihar Ogun.

Sai dai kuma Amosun ya ki bin shawarar Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro, inda ya wuce makadi da rawa, ya shigo da dimbin bindigogi da harsasai.

Jama’a da dama da masu rajin kare jama’a dama kungiyoyi dai na ta rajin kiraye-kirayen a kama Amosun a hukunta shi.

Share.

game da Author