Hukumar Kula da Yiwuwar Barkewar Amabaliya ta bayyana cewa jihohi biyar na kasar nan na cikin halin tsammanin barkewar ambaliya. A bisa wannan dalili ne gwamnati ta ce jami’an ta da sauran al’umma su yi kaffa-kaffa.
Babban Daraktan Hukumar Mai Suna Clement Eze ne ya bayyana haka a Abuja, inda ya lissafa jihohin Edo, Rivers, Anambra da Bayelsa cewa su ne jihohin da ake jiran tsammanin barkewar wannan ambaliya.
Idan za a iya tunawa, cikin watan Oktoba na 2012, an yi mummunar ambaliya a jihohin Delta, Rivers, Anambra da kuma Bayelsa din.
A lokacin har shugaban da ke kan mulki, Goodluck Ebele Jonathan ya karade kasar nan, ya na yawon rangadin dubiya da jaje a jihohin duk da ambaliya ta yi wa ta’adi.
A jiya Litinin kuma, Eze ya bayyana cewa ambaliyar ta yi kaca-kaca da wasu sassan jihohin Adamawa, Taraba, Benuwai da Kogi.
Ya kuma kara cewa akwai yiwuwar barkewar ambaliyar a Edo, ddelta, Anambra, Rivers da Bayelsa.
Daga nan ya fito karara ya kara da cewa balle Madatsar Ruwa ta Lagdo da Gwamantin Kamaru ta yi a ranar 10 zuwa 31 ne musabbabin ambaliya a Arewacin kasar nan.
“Bayan Kamaru ta bata makonni da yawa ta na musanta zargin cewa ta balle madatsar ruwan, a karshe dai ta tabbatar wa Najeriya cewa ta balle ruwan domin dam din ya cika ya tumbatsa, gudun kada ya yi ambaliya cikin kasar ta.”
Ya kuma kara danganta yiwuwar hakan sakamakon yadda ruwan sama ta dade bai dauke ba.
“Bayan ambaliyar 2012 wadda ta ragargaza Najeriya , kasashen Najeriya da Kamaru sun rattaba yarjejeniyar cewa kasar Kamaru za ta rika bayar da isasshen lokaci da kuma sanarwa da wuri na lokacin da za ta balle dam din Lagdo, saboda idan aka balle dam din, ruwan kan kwararo har cikin Najeriya.
Don haka Eze ya ce daga ranar 3 Ga Nuwamba 2019, har ruwa ya kai ma’aunin 11.28m a Kogin Benuwai. Hakan kuwa akwai firgita ne da barazana sosai, domin ko ambaliyar 2012 da aka yi, ruwan da ya cika Kogin Benuwai bai wuce ma’aunin 9.01 a ranar 4 Ga Nuwamba, 2012 ba.
Ya kuma ce a yanzu haka Dam din Kainji na fama da ruwan da ya wuce misali.
Discussion about this post