Akalla matata miliyan 6.5 ne ke amfani da dabarun bada tazarar iyali a Najeriya – Binciken FP 2020

0

Sakamakon binciken da kungiya mai zaman kanta ‘Family Planning 2020(FP2020)’ ta gudanar ya nuna cewa mata miliyan 6.5 ne ke amfani da dabarun bada tazaran iyali a Najeriya.

Binciken ya cewa an samu karuwar yawan mutane da ke amfani da dabarun bada tazarar iyali a wasu kasashen duniya masu tasowa guda har 68.

An gabatar da wannan sakamako ne a taron da kungiyar ta shirya da aka yi a Kasar Nairobi.

Idan ba a manta ba a shekarar 2012 ne aka kafa FP2020 domin inganta kiwon lafiyar mata ta hanyar wayar musu da kai don sanin muhimmancin amfani da dabarun bada tazarar iyali na zamani.

Shugaban kungiyar Beth Schlachter ta bayyana cewa an samu ci gaba a kasashen duniyan da suka hada kawance da su musamman Najeriya.

Schlachter ta ce binciken da suka gudanar a Najeriya ya nuna cewa a dalilin amfani da dabarun bada tazarar iyali mata akalla miliyan 2.3 basu daukar ciki na gaira babu dalili kamar da. Sannan a wannan shekara na 2019 an samu karin mata miliyan 9 da ke amfani da dabarun tsara iyali.

Ta kuma ce hakan ya sa an samu nasarar hana mata 800,000 zubar da ciki musamman ta hanyoyin da basu dace ba, sannan a shekarar 2018 an ceto rayukan mata 13,000 a wajen haihuwa.

Schlachter ta ci gaba da cewa har yanzu akwai aiki da dama a gaban su wajen wayar da kan mutane game da alfanun dake tattare da bada tazarar iyali.

Ta ce a yanzu haka akwai mata kashi 23.7 bisa 100 da har yanzu basa amfani da dabarun.

Sannan a duk kasashen Afrika Najeriya it ace kasar da bata samun ci gaba sosai domin a yankin gabas da kudanci Afrika an samun ci gaban kashi 7 bisa 100.

Schlachter ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara zage damtse wajen ganin ta samar da dabarun bada tazaran iyali ga mata da ‘yan mata a kasar nan.

Ta ce yin haka zai taimaka wajen inganta kiwon lafiyar mata sannan da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Idan ba a manta ba a watan Satumba wani kungiya mai zaman kan sa mai suna ‘Marie Stopes International Organinsation Nigeria (MSION)’ ya yi kira ga gwamnatocin duniya da su wadatar da dabarun bada tazarar iyali ga duk matan dake bukata.

Shugaban kungiyar ‘MSION’ Effiom Effiom ya ce wayar da kan mata ya zama dole ganin cewa har yanzu mata akalla miliyan 214 dake bukatan dabarun bada tazaran iyali basu iya kaiwa ga shi.

Effiom yace domin samar da tallafi kungiyar su na bai wa matan dake bukatar dabarun bada tazarar iyali kyauta a Najeriya.

Share.

game da Author