Afenifere ta gargadi masu ji-ta-ji-tar neman zarcewar Buhari zango na uku

0

Kungiyar Kare Mutuncin Siyasar Yarabawa zalla mai suna Afenifere, ta yi kira ga ‘yan Najeriya cewa su sa ido sosai, dangane da yada ji-ta-ji-tar neman zarcewar Shugaba Muhammadu Buhari a zango na uku.

Daga nan kuma kungiyar ta yi tir da Majalisar Dattawa saboda bata lokacin da Afenifere ta ce majalisar na yi har ta ke tattauna batun kudirin dokar kalaman kiyayya.

Afenifere ta ce wannan kudiri ne mai neman tauye wa jama’a ‘yancin magana.

Bayan Afenifere ta tashi daga wani taron ta jiya Talata, a Akure, kungiyar ta tunatar da jama’a cewa maganar zarcewar Buhari a zango na uku ta faro ne tun lokacin yakin neman zabe, inda wani dan takarar sanata a Jihar Bauchi ya bayyana cewa shi zai nemi sake komawa Majalisar Dattawa ce don kawai su kitsa tuggun da za a yi wa doka kwaskwarima, ta yadda za ta amince wa Buhari ya yi zango uku, maimakon biyun da doka ta kayyade masa.

“Daga nan kuma sai wani subul-da-baka da Shugaba Buhari ya yi, inda ya ce zai fitar da mutane milyan 100 daga cikin kangin talauci, a cikin shekaru 10.”

Afenifere ta tunatar wa jama’a cewa shekara takwas dai ce dokar Najeriya ta amince Buhari ya yi a kan mulki, to amma ga shi ya na cewa ‘a cikin shekara 10.

Afenifere ta ce duk da dai Buhari ya fiton ya musanta cewa ba zai yi tazarce ba, to ba za su yi saurin amincewa da shi ba, saboda ba karon farko ba a can baya Buhari ya sha karya alkawarin da ya dauka.

“Saboda ba za mu manta da cewa Buhari ya yi alkawari cikin 2011 ba, wanda ya ce idan ya samunshugabancin Najeriya, to zango daya kadai zai yi.

“To ya karya wannan alkawarin, sannan kuma a cikin 2015 ya yi alkawarin ba zai kirkiri ofishin Uwargidan Shugaban Kasa ba. Shi ma ya kirkiro shi daga baya, har ma ya nada mata hadimai guda shida.

Daga nan sai Afenifere ta ce doka ce ta hana Buhari yin tazarce. “Shin idan aka yi wa dokar kwaskwarima, aka kafa wadda ta amince masa yin zango na uku kuma fa?”

Daga nan Afenifere ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su ruka zuba ido sosai, don kada a yi musu sakiyar da babu ruwa.

Sannan kuma ta yi kira ga Buhari da ya tashi ya gudanar da ayyukan inganta al’umma, yadda zai bar bayan sa ta zama abin yabo, ba abin yi wa tir da assha ba.

Share.

game da Author