3-1: Liverpool ta wujijjiga Manchester City

0

An shafe mintina 94 ana gumurzu, gwagwagwa, gwangwa-da-gwangwa, gurugubji lailaya kwallo tsakanin gwanayen Ingala biyu, Liverpool da Manchester City, a wasan da masu masaukin baki, Livrrpool suka yi wuji-wuji da City da ci 3:1.

Tun a farkon fara wasan daidai minti 6, dan bayan Liverpool Firbinho ya kwanta kwance-kwance daga nesa ya kwarara kwallo cikin ragar Manchester City, inda nan take ‘yan kallo cike da filin wasan Anfield suka barke da ihu.

Minti 7 bayan cin kwallo ta farko, daidai minti na 17 kuma hatsabibin dan wasa Mohamed Salah ya dama wa Manchester City kunun salala mai zafi, inda ya afka musu kwallo a cikin raga ta hanyar jefa da kai.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ba da dadewa ba, daidai minti na 51 shi ma Sadio Mane ya yi shigar karimtsa-da-rimatso a cikin yadi na 18, inda ya bi kwallo ya jefa ta a ragar Manchester City da kai.

‘Yan wasan City irin su Raheem Sterling da Kun Aguero sun yi bajintar neman fitta kunya, amma da kyar aka jefa wa Liverpool kwallo daya a raga.

Duk da an jefa wa Man City kwallaye 3, sun rika buga kwallo kamar ran su zai fita, da nufin rama kwallayen su.

A yanzu dai an yi wasanni 12, inda Liverpool ke da maki 34. Wato ta tsere wa City da maki 9.

Kafin a fara wasan dai kpcoyan nan mai daukar Dala da gammo hayaniya, Jose Mourinho, ya ce idan Liverpool ta yi nasara a kan City, to ita za ta dauki Kofin Premier na 2019/2020.

Share.

game da Author