2023: Za mu bi tsarin jam’iyya sau-da-kafa wajen zaben dantakarar shugaban kasa don gudun kada aji Kunya – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa jam’iyyar APC zata tabbata ta bi dokar jam’iyyar wajen zabin dantakarar shugaban kasa a 2023.

Buhari ya furta wannan kalamai ne a ranar Juma’a a wurin Taron Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar APC, a Abuja.

” Idan muka bari APC ta ruguje bayan 2023, ba mu yi wa jam’iyyar adalci ba. Dole mu bi tsarin dokar jam’iyyar sannan a rika yi wa jam’iyya da’a. Ko kadan ba mu ji dadin abubuwan da suka faru a jihohin Imo, Bauchi da Zamfara a 2019.

” Dole sai an zabi shugabanni nagari tun daga zaben mazabu har zuwa mataki na kasa sannan za a samu natsuwa da ci gaba da kuma bin tsarin doka.

Buhari yayi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su daina bin ra’ayinsu ko nuna son kai da kin bin abinda tsarin dokar jam’iyyar ya ce.

Bayan haka Shugaba Buhari ya yi watsi da surutan da ya ce ana watsawa da ake danganta shi da yunkurin yin tazarce a 2023, idan ya kammala halastaccen zangon sa na biyu.

Buhari ya ce ba zai taba yin tazarce ba, kuma ba shi da wannan niyya a boye a zuciyar sa.

“Ba ba zan taba ganganci ko tafka kuskuren neman yin tazarce ba.

“Baya ga doka ta ba ni damar yin zango biyu kadai. Sannan kuma banda cewa ga tsufa ya cim min, na kuma rantse da Alkur’ani cewa zan bi ka’idojin da dokar kasa, kwansitushin ta tsaya. Don haka ba zan karya wannan rantsuwa ba.

“A yanzu tsufa ya kama ni, kuma ina kan zango na biyu, wanda shi ne na karshe da doka ta amince min. Don haka ba zan yi kuskuren nan yin zango na uku ba. Ba zan sake neman kuri’ar kowa a kasar nan ba.”

Share.

game da Author