2023: Buhari ya ce ba zai nemi yin tazarce ba

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da surutan da ya ce ana watsawa da ake danganta shi da yunkurin yin tazarce a 2023, idan ya kammala halastaccen zangon sa na biyu.

Buhari ya ce ba zai taba yin tazarce ba, kuma ba shi da wannan niyya a boye a zuciyar sa.

Buhari ya furta wannan kalami jiya Juma’a a wurin Taron Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar APC, a Abuja.

“Ba ba zan taba ganganci ko tafka kuskuren neman yin tazarce ba.

“Baya ga doka ta ba ni damar yin zango biyu kadai. Sannan kuma banda cewa ga tsufa ya cim min, na kuma rantse da Alkur’ani cewa zan bi ka’idojin da dokar kasa, kwansitushin ta tsaya. Don haka ba zan karya wannan rantsuwa ba.

“A yanzu tsufa ya kama ni, kuma ina kan zango na biyu, wanda shi ne na karshe da doka ta amince min. Don haka ba zan yi kuskuren nan yin zango na uku ba. Ba zan sake neman kuri’ar kowa a kasar nan ba.”

Sai sai kuma duk da wannan kalami da Shugaba Buhari ya yi, jama’a da dama ba su amince masa ba, duba da yin la’akari da alkawurran da suka ce ya karya a baya.

Alkawurran Da Buhari Ya Karya

A cikin 2014 dai Buhari ya yi alkawarin cewa idan ya hau mulki, zango daya kadai zai yi. Jaridu da dama sun buga wannan labari, har ma da kafafen yada labarai na waje.

Sannan kuma bayan ya ci zabe cikin 2015, jaridar Trust ta buga labarin yadda Buhari ya je Daura, ya tara dangi, ya ce ba zai bari ‘yan uwa su rika yi masa tururuwa zuwa Fadar Shugaban Kasa ba.

Wannan ma bai cika ba, domin ya dauko dan babban yayan sa, Mamman Daura, ya ba shi gidan zama a cikin Villa har da iyalin sa.

Idan ba a manta ba, cikin watan da ya gabata, an fallasa wani bidiyo na wata hayaniya da ta faru tsakanin matar Buhari, Aisha, tare da iyalan Mamman Daura a cikin Villa.

Na uku kuma Buhari ya ce ba zai yi wa Aisha Ofishin Uwargidan Shugaban Kasa ba.

Amma sai ga shi daga baya ya daukar ma ta hadimai masu yawa, tare da na matar mataimakin sa Yemi Osinbajo a asirce.

Na hudu, Buhari ya sha alwashin cewa idan ya hau mulki zai saida jiragen Fadar Shugaban Kasa, ya bar biyu kadai.

Wannan ma bai cika ba, sai ma karin kudi da aka gano an yi da za a rika kashewa wajen kula da jiragen.

Shi ya sa da yawa ba su gamsu ba da alkawarin da ya dauka a jiya Juma’a, cewa ba zai nemi tazarce a 2023 ba.

Share.

game da Author