Wasu ma’aikatan Hukumar Kula da Aikin ’Yan Sanda ta Kasa (Police Service Commission), sun fito sun yi wa rundunar ’yan sanda zanga-zanga, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Sun yi musu zanga-zangar ne domin nuna rashin amincewa da harkallar da ake zargi ’yan sanda sun tafka wajen daukar sabbin kurata 10,000.
Ana zargin Shugaban ’Yan sandan kasar nan Adamu Muhammad da wannan badakalar.
Masu zanga-zangar dai sun fito ne a karkashin inuwar Kungiyar Ma’aikatan Gwamnatin Najeriya Reshen Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda.
Sun rika daga kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce daban-daban akan Sufeto Janar da sauran su.
Sun kuma rika rera wakokin adawa da yadda aka yi daukar sabbin kuratan ‘yan sandan, wanda aka ce an yi harkalla sosai a ciki.
An gudanar da zanga-zangar ce a daidai lokacin da Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya, Inyang Ekwo, ya zartas da hukuncin soke dukkan sunaye 10,000 da aka dauka aikin dan sanda.
Sakataren kungiyar ma’aikatan, Remi Ogundeji, ya shaida wa manema labarai cewa su na zanga-zangar ce domin nuna rashin yarda da kwacen ikon daukar sabbin kuratan ‘yan sanda a Rundunar ‘Yan Sanda a karkashin Sufeto Janar Adamu ta yi wa Hukumar Daukar ‘yan sanda.
A yanzu dai kotu ta umarci Sufeto Janar da a dakatar da daukar kuratan ‘yan sandan tukunna.
Wasu kafofin yada labarai sun ruwaito cewa wasu jihohi sun nuna rashin amincewa da yadda aka dumbuza wa jihar Nasarawa gurrabun daukar kuratan ‘yan sanda fiye da kowace jihar a kasar nan, banda Katsina, jihar da Shugaba Muhammadu Buhari ya fito.
Nasarawa ita ce jihar Sufeto Janar Adamu Mohammed ya fito.