ZABEN KOGI: Ko Sanata Dino zai tsallake wannan siradi?

0

Hukumar Zabe ta bayyana ranar 16 ga watan Nuwamba a matsayin ranakun da za a sake zaben kujerar sanata ta Kogi ta Yamma.

Idan ba a manta ba kotun koli ta soke zaben shiyyar wadda sanata Dino yake wakilta.

Sanata Adeyemi Smart na APC ne ya kalubalanci nasarar da Dino na jam’iyyar PDP yayi a zaben 2019 kuma yayi nasara a Kotu.

Dino dai ya na cikin tsaka mai wuya domin a wannan rana ne za a yi zaben gwamnan Kogi wadda APC da gwamna mai ci Yahaya Bello tuni har sun wasa wukaken su domin yi wa PDP yankan rago.

Wannan rana ba zai yi wa Dino dadi ba domin kuwa akwai alamun cewa wa’adin sa a kare yanzu kam a ci gaba da wakiltan mutanen Kogi ta Yamma.

Za a gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa ranar 16 ga watan Nuwamba.

Yadda Dino zai ci zabe a Kogi

Da yake zaben za a yi shi ne tare da na gwamnan jihar, akwai yiwuwar hankalin gwamnan na sa kujerar zai fi maida hankali akai da hakan ya iya yi wa Dino tasiri.

Sai dai kuma ita ma wannan yanki na Kogi ta Yamma Yahaya na bukatar ta don cin zabe.

Baya ga haka, Sanata Dino na da saura farinjini a wannan shiyya da wasu ke ganin ya ma fi Smart na APC.

Matasan shiyyar za su yi wa Dino ruwan kuri’u musamman ganin yadda yake tare da su tun farkon siyasar sa.

Yanzu da shawara ya rage wa mai shiga rijiya. Ko ya shiga ta kai ko a tsaye sambal, ranar wanka dai ba a boye cibi.

Ko Dino zai koma ya ci gaba da yi wa ubangidan sa Sanata Bukola Saraki dan koro ne ko kuma za a ci gaba da damawa da shi a wannan majalisa?

Share.

game da Author