ZABEN KANO: Yadda kotu ta kayar da Abba Gida-gida

0

Kotun Daukaka Karar Zaben Gwamnan Jihar Kano, ta tabbatar wa Gwamna Abdullahi Ganduje nasarar zaben da INEC ta sanar shi ne ya yi nasara.

Da ta ke karanta hukuncin shari’ar, wadda ta shafe awa hudu ta na jawabi, shugabar alkalan uku, Halima Shamaki ta ce babu wata tantama Ganduje ne na APC ya yi nasara a kan mai shigar da kara, Abba Kabir Yusuf na PDP.

Don haka ta ce ba ma tare da dogon bayani ba, ta kori karar domi PDP da Abba sun kasa gabatar da hujjojin cewa an tabka magudi ko na daidai ba a lokacin zabukan.

Shamaki ta ce dukkan alkalan su uku sun gamsu cewa INEC ta yi daidai da ta bayyana zaben gwamna a ranar 9 Ga Maris, cewa bai kammalu ba.

Sannan kuma sun gamsu da yadda INEC ta bayyana cewa Ganduje ne ya yi nasara a zaben cike gurbin zaben mazabu na ranar 9 Ga Maris.

Halima ta ce batun da PDP da Abba suka yi ikirarin wai su ne suka yi nasara, kawai tatsuniya ce, abu ne ba karbabbe ba, kamar ka hada ruwa da mai.

Ta ce masu kara sun kasa kawo hujjojin cewa an tabka magudi ko an yi tashe-tashen hankula a lokacin zabe.

Shugaban J’am’iyyar PDP na Jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi, ya ce za su je su yi Mazarin hukuncin da kotu ta bayar, sannan su san matakin da za su dauka a gaba.

Shi kuma Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Abbas, cewa ya yi kotu ta yi daidai.

Share.

game da Author