ZABEN 2019: Kotun koli zata sake Sauraren korafin jam’iyyar Hope

0

Kotun Koli ta bayyana cewa za ta sake zama domin sake duba korafin da jam’iyyar Hope ta shigar na kalubalantar hukuncin da kotun ta yanke akan karanta.

Idan ba a manta ba Kotu ta yanke hukunci akan karar da jam’iyyar Hope ta shigar tana kalubalantar dage zaben shugaban kasa da aka yi daga 16 ga watan Faburairu.

Jam’iyyar Hope ta ce yin haka da hukumar zabe ta yi karya dokar kasa ce sannan da kuma yadda kotu ta yanke hukunci akan batun da ta shigar a gabanta.

Kotun koli ta ce lallai ta amince ta sake zama domin yin nazari akan wannan kara da hukuncin da aka yanke a wancan lokaci.

Kotu ta ce za tayi wannan zama ne ranar 28 ga watan Oktoba.

Jam’iyyar Hope ta ce baya ga sake duba wannan hukunci da aka yanke a baya, ta na neman kotu ta bayyana ta a matsayin jam’iyyar da ta yi nasara a zaben shugaban kasa.

” A dalilin wannan kuka da muka mika ina so in tabbatar muku cewa mun yi zaben jin ra’ayin mutane kuma jam’iyyar Hope ta samu akalla kuri’a miliyan 50 da haka ya sa muke nema kotu ta bayyana mu jam’iyyar da ta yi nasara.

Share.

game da Author