Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana cewa zata gina rugagen Fulani 57 a sassan jihar domin rage yawan tashin hankali da rikici dake barkewa a tsakanin makiyaya da manoma a jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Umaru Namadi ya sanar da haka a wani zama da aka yi da jami’an tsaro a jihar.
Namadi yace gwamnati za ta gina rijiyoyin burtsatse a duk wadannan rugaggen sannan ta raba baburan hawa guda 62 wa shugabanin makiyaya Fulani da manoma a jihar.
Ya yi kira ga manoma da makiyaya Fulani da su gujewa yi wa doka karan tsaye a jihar, yana mai cewa su rika zama da juna lafiya.
Kwamishian ‘yan sandan jihar Bala Sanchi ya bayyana cewa ci gaban kowani kasa ya dogara ne da zaman lafiya a kasa. Saidai hakan ba shine ke faruwa ba a jihar ba saboda matsalar rashin jituwa tsakanin Fulani da Makiyaya.
Idan ba a manta ba a watan Agusta ne gwamnatin jihar Zamfara ta tsayar da ranar 2 zuwa 6 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a aza tubalin ginin alkaryar RUGA a jihar da kuma kaddamar da ita kanta wannan katafaren fili da aka kebe domin haka.
Gwamnati za ta raba takin zamani a wasu garuruwan Fulani,bada magunguna kyauta, gina makarantun firamare, asibitoci domin makiyaya sannan za a gina dam-dam na ruwa domin dabbobin makiyaya a wadannan rugage.