Kwamishian kiwon lafiya na jihar Anambra Vincent Okpala ya bayyana cewa ma’aikatar kiwon lafiya zata kafa cibiya da zai rika kula da mutanen da suka ji rauni a dalilin hadarin mota, gobara da rushewar gini a jihar.
Okpala ya ce yin haka zai taimaka wajen rage yawan mace-macen mutane da dama a dalilin ire-iren wadannan hadarukka.
Okpala ya kara da cewa yin haka ya zama dole domin ceto rayukan mutanen dake fadawa cikin irin wannan matsala.
Bayan haka opala ya koka da rashin kudade da ma’aikatar ke fama da su da ya rage aiyukkan ma’aikatan zuwa kashi 18 bisa 100 .
Ya yi kira ga kwamitin da ta hanzarta tantance kasafin kudin 2020 domin aiki ya kankama.
Discussion about this post