‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 6 da malamai 2 a makarantan kwana a Kaduna

0

Wasu ‘yan bindiga sun arce da ‘yan mata shida da malamai 2 a wani makarantar kwana mai suna Engravers College da ke unguwar Sabon Tasha dake Kaduna a daren Laraba.

Ma’ajin makarantar Elvis Allah-Yaro ya bayyana cewa hukumar makarantar ta sanar wa ‘yan sanda da tuni har an aika jami’ai subi sahun wadannan masu garkuwa.

Hukumar makarantar sun tabbatar da yin garkuwa da dalibai 6 da malamai 2. Sannan ta bayyana cewa maharan sun far wa makarantar ne da misalin karfe 12:30 na daren Laraba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Yakubu Sabo bai amsa kira da wakilin PREMIUM TIMES yayi masa ba.

Share.

game da Author