Yadda ‘Yan Mata ke fadawa cikin kangin malamai a jami’o’in kasar nan, Daga Kais Daud Sallau

0

Babu shakka ‘yan mata dalibai na fadawa cikin tashin hankali a lokacin da suka tafi makarantan gaba da sakandare (secondary) kama daga jami’a koleji da sauransu.

Dalibai matan sukan haduwa da tashin hankalin ne lokacin da Allah ya hadasu da wani malami (Lecturer) mara tsoron Allah, wanda shi burinsa ko da yaushe ya rika amfani da daman da yake dashi don bata tarbiyan yaran matan. Wallahi wata yarinyar zaka ga iyayenta sun turo ta makaranta ba tare da tasan namiji ba, amma malami zaiyi amfani da damar da yake dashi ya bata mata rayuwa ba tsoron Allah.

Kais Daud Sallau

Kais Daud Sallau

Wadansu daga cikin gurbatattaun malamai gaba da ire-iren wadannan makarantu (Lecturers) suna yi wa dalibai matan barazana ne da ko su basu kansu kokuma su kayar dasu a darasin (course) da suke koyar dasu ko sun rubuta abinda ya kamata a ce sun ci wannan darasin.

Hakan yasa wadansu dalibai matan saboda tsoron kada malamin (lecturer) ya kayar da su sai su sakanwa wannan malamin kansu yayi amfani dasu domin su ci darasin (course) na wannan malamin.

Zaka ga yarinya tayi duk abinda ya kamata ta ci jarabawa, amma saboda taki ta baiwa wannan malamin kanta yayi iskanci da ita sai ya kayar da ita. Haka zaka ga wata bai kamata ta ci jarabawa ba saboda ba abinda da rubuta, amma saboda ta sakar wa wannan malamin kanta yayi iskanci da ita, sai ya bata ci.

Su kuma yaran matan suna tsoron su kai karan malamai gurin hukumar makaranta saboda malamai suna yi musu barazanan cewa, zasu sa a koresu a makaranta idan har suka nima su tona musu asiri tunda basu da hujjan da zasu nunawa hukumar makarantan.

Wannan abune wanda duk dan Najeriya yasan yana faruwa a makarantar gaba da Sakandare, abin ya zama ruwan dare kusan duka makarantun da muke dasu ana samun wannan abin.

Ya kamata malam (lecturers) su ji tsoron Allah, susan cewa wadanda yaran da iyayensu suka turo su makaranta amana ne gare su. Ya kamata susan cewa kyakkyawan tarbiya a matsayinau na malamai ya kamata su nunawa dalibarsu bawai suyi amfani da damar da suke dashi su ci amanar dalibansu, su kuma ci amanar iyayen dalibansu da suka basu amanar yarinyansu ba.

Sannan ya kamata duk malamin (lecturer) da aka kamasa da irin wannan ta’asa, ba wai koransa daga aiki kadai ya kamata ayi ba.

Bayan an koresa, ya kamata ayi wani doka wanda zaa mishi hukunci mai tsanani (a tura shi gidan yari) tare da kuma haramta masa yin aiki a duk wani makaranta gaba da Sakandare (secondary). Domin ba shakka wallahi akwai gurbatattun malamai da idan banda bata tarbiyan yara ba abinda suke yi.

An kai matsayin da har luwadi suna yi da dalibai maza. Ya kamata hukuncin yayi aiki akan malamai masu yin luwadi da dalibai su. Domin shima yanzun ya zama ruwan dare a makarantun gaba da sekondiri (secondary).

Bai kamata ace an same wani malami da irin wannan cin zarafi ace wai koransa kawai daga aiki shine hukuncin da zaayi masa ba. Domin gadaransu ko an koresu a wannan makarantan, zaa sake daukansu a wani makaranta. Amma idan akayi dokan da zaa kaisa gidan yari, sannan a haramta masa yin aiki a wani makarantan gaba da sekondiri (secondary), toh dayawansu zasu yi hatara da wannan mummunan dabi’ar.

Bai kamata ace mahukunta su zuba ido ana lalata yaran mutane ba wani matakin azo a ganin da ake daukawa akan masu aikata wannan miyagun aikin ba. Wannan dabi’ar yana daya daga cikin abinda ya kara lalata harkan ilmi a kasan nan. Toh yarinya ba abinda ta sani amma saboda malamai na yin iskanci da ita sai ta kare da sakamako mai kyau. Sai taje wani gurin an nima ta kare wannan karatun nata, sai ta gagara.

Ina kuma bawa yaran matan shawara, duk wani malami da ya nima yayi iskanci dake, kiyi kokari ki tara ingantattun hujjoji da zaki iya kare kanki dashi.

Idan akwai hujja kada kiji tsoron komai, ki tona masa asiri. Idan kuma hukumar makaranta basu dauki mataki ba, ki tallata a duniya. Zamu tayaki har sai an dauki mataki da ikon Allah.

Haka kuma dalibai maza, duk malamai da ya nema yayi luwadi daku, ku tara ingantattun hujjoji kawai, sai a tona masa asiri.

Allah ya bamu zaman lafiya a Nigeriya. Allah ya shiryar damu, ya kuma shiryar da malamai masu irin wannan halin, idan kuma ba masu shiryuwa bane, Allah kayi mana maganinsu.

Share.

game da Author