Karamin Ministan Harkokin Man Fetur, Timipre Sylva, ya bayyana damuwa dangane da yadda Najeriya ke kashe makudan kudade wajen hako danyen man fetur.
Sylva ya ce tilas a tashi tsaye a lalubo hanyoyin da za a bi domin rage tsadar hako danyen man fetur a kasar nan.
Ya ce idan aka yi haka, za a kara samun rarar makudan kudaden shiga a cikin aljihun gwamnatin tarayya, wadanda za ta rika amfani da su ta na aiwatar da ayyukan raya kasa da inganta tattalin arziki.
Minista Sylva ya yi wannan bayani ne jiya a Abuja, wurin Taron Gano Dabarun Rage Tsadar Hako Danyen Mai a Najeriya, wanda Hukumar PTDF da QSRBN suka shirya.
Sylva wanda Shugaban Ma’aikata na Ma’aikatar sa, Moses Olamide ya wakilta, ya bayyana cewa a halin yanzu Najeriya sai ta kashe dala 35 kafin ta hako kowace gangar danyen man fetur daya jal. Wannan kuwa ya ce ba abu ba ne mai dorewa.
“Bari na dan yi waiwayen baya. Cikin shekarun 1980 zuwa shekarun 1990, Najeriya na kashe dala 4 kadai wajen hako kowace ganga daya ta danyen mai.
“Cikin shekarun 2000 kuma tsadar ta dan daga zuwa dala 5. Amma a yanzu tsadar ta yi munin da sai an kashe akalla dala 35 kafin a iya hako kowace ganga daya ta danyen man fetur a kasar nan.”
Sylva ya nuna takaicin yadda Najeriya ke kashe makudan kudade wajen hako danyen mai, alhali kasashe kamar Kuwait da UAE su na kashe dala 10 kadai wajen hako kowace ganga daya.
“Don haka a wannan lokacin da ake sayar da kowace ganga daya a kan dala 50 zuwa 60, bai yiwuwa a ci gaba da kashe dala 35 kafin a hako kowace ganga daya ta fetur.” Inji Sylva tare da yin kira a lalubo wasu hanyoyin da za a rage tsadar hako danyen mai a Najeriya.