Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyanawa taron gwamnonin Najeriya yadda babban darektan Bankin Duniya a Najeriya mai barin gado ya taimaka masa ya samu bashin zunzurutun kudi har dala miliyan 350 daga bankin duniya.
El-Rufai ya shaida wa taron cewa bayan darewar sa kujerar gwamnan jihar Kaduna, ya fuskanci matsalar rashin makarantun arziki a jihar.
Ya ce makarantun jihar duk sun lalace da hakan ya rika tada masa da hankali sannan ya rasa yadda zai yi. ” A haka ne na rika tara hotunan wadannan makakarantu daga nan na garzaya kai tsaye zuwa ofishin babban darektan Bankin duniya a Najeriya wato Rachid Ben Massaoud domin neman agaji.
” Bayan mu tattauna sannan ya fahimci irin matsalolin da muke fama da su a jihar Kaduna musamman wajen inganta Ilimi sai ya bani shawarar yadda zan bi in samu wannan bashi daga bankin duniya inda a karshe dai na samu suka bani bashin.”
Daga nan sai na shawarci wasu gwamnoni ‘yan uwana da su yi kwaikwayi abinda na yi cewa Rachid Ben Massaoud zai taimaka musu muddun suna da abinda za su iya nunawa domin samun bashin daga bankin duniya domin gyara jihohin su.
Gwamnonin da suka halarci wannan taro sun yabawa babban darektan mai barin gado Rachid Ben Massaoud suna masu cewa ba a taba yin kamar sa ba a Najeriya.
” Ba kai ne babban darekta na farko ba ada aka turo wannan Kasa, amma dai salon mulki ya dare na sauran a dalilin irin gudunmuwar da ka rika ba gwamnoni domin ci gaban jihohin su.” Inji Shugaban gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi.
Discussion about this post