Yadda matashi ya waske da Naira 670,000 kudin zakka da sadaka a coci

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wani matashi mai shekaru 18 mai suna Elikor Ehud da laifin sace kudaden sadaka da zakka da mutane suka tara a cocin ‘Chosen Vine Ministry, Furniture Avenue’ dake Ejigbo a jihar Legas.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Bala Elkana ya bayyana haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a Legas.

Elkana yace faston cocin Moses Nwoke ne ya kawo karan wannan matashi ofishin ‘yan sandan dake Ejigbo bayan an gano abinda yayi.

“Nwoke ya ce ya gane cewa kusan baki daya kudaden sadaka da zakkan da mutane suka tara a coci an sace su saura dan kadan a cikin kwandon sadakan.

“Nan da nan kuwa ya garzaya ofishin mu ya sanar da mu.

Elkana yace da suka kama barawon ya tabbatar da shine ya wawushe kudin.

Ehud ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya aikata wannan aika-aika ne da taimakon wani abokinsa mai sun Lucky wanda har yanzu ‘yan sanda na neman sa ruwa a jallo.

Elkana yace da zaran sun kammala bincike za a maka Ehud a kotu.

Share.

game da Author