Rashin sani ya sa sani babban malamin Jami’ar Legas kokarin yin lalata da wata yarinya da ta je a matsayin mai neman a dauke ta shiga jami’ar.
Boniface Igbeneghu bai san cewa Kiki Mordi ba CE, ‘yar jarida mai aiki da BBC Africa, ta yi basaja, a matsayin daliba mai neman shiga makarantar.
Sannan kuma bai san cewa duk abin da ya yi mata ba na kokarin yin lalata da ita, ta rika daukar bidiyon sa.
BBC Africa sun yi wannan binciken ne a kokarin gano zargin lalata da dalibai mata ana ba su maki ko a dauke su da ake ta zargin na faruwa a jami’o’in Afrika ta Yamma.
Baya ga babban malamin jami’a, Boniface fasto ne a Cocin Foursquare Gospel Church.
Da farko bayan ya kai ta ofis, ya fara tambayar ta “shekarun ki nawa ?”
Ta ce masa shekarun ta 17. Sai ya ce, “kin kuwa san irin kyan da ki ke da shi? To ni dama irin ku na ke so ‘yan shila. Kun fi dadin sha’ani.”
Bayan nan ya sake kiran ta karo na biyu a ofis din sa, inda ya sa ta zauna su ka yi addu’a.
Bayan gama addu’a ya ce ma ta akwai wurin da malaman jami’ar ke daukar dalibai mata ana zuwa ana hutawa.
“Ina fatan ke ma duk abin da za mu yi, kada ki bari mahaifiyar ki ta sani.”
A karo na uku ne ya fito ya ce ma ta idan fa ta na so bukatar ta ta biya, to sai ta ba shi hadin kai. Bayan ya shiga ban daki a cikin ofis din sa ya fito, sai ya kashe wuta, ya nufe ta ya kama ma ta nonuwa.
Boniface duk bai san ta na daukar bidiyon da da maganganun sa ba.
An yi ta watsa bidiyon a BBC Africa Sashen Yarabanci. Kuma Premium Times ta ga bidiyon.
An tuntubi jami’ar yada labarai na Jami’ar Legas, Taiwo Oloyede, ya ce malaman jami’ar ba lalatattu ba ne. Kuma jami’ar ba ta lamuntar lalataccen malami.