Shugaban Amurka Donald Trump ya bada sanarwar nasarar da sojojin Amurka suka yi wajen kashe shugaban ‘yan ta’addar ISIS, Abubakar Al-Baghdadi.
Da ya ke jawabi cike da farin ciki da tinkahon babbar nasara daga ofishin sa a Fadar Amurka ta White House, Trump ya ce “an aika da mugun iri lahira” a kwanton-baunar da aka yi masa a Arewacin kasar Syria.
Trump ya ce, “sojojin Amurka ne suka darkake shi, bayan da ya shiga cikin wani wawakeken bututu, sai suka cunna masa karnuka suka far masa.”
“Yayin da ya ga an kure masa gudu, sai Al-Baghdadi ya tada bam da ke manne a jikin wata rigar sulken sa.
” Bam din ya kashe har da wasu ‘ya’yan Al-Baghdadi din su uku. Kuma yayin da aka bi shi, ya rika kwartsa ihu ya na raki, tamkar wani matsoraci.” Inji Trump.
Shugaban na Amurka ya ce wannan babbar nasara ce, kuma za a nuna wa duniya yadda aka yi masa kisan wulakanci, don matasa masu gangancin son shiga harkar ta’addanci su sha jinin jikin su.
Al-Baghdadi ya kafa kungiyar ta’addancin ISIS, cikin 2010, inda ya yi huduba a babban masallacin Juma’a mai tarihi da ke Mosul, ya ce shi ne sabon Sarkin Musulmin dukkan kasashen Larabawa da Gabas ta Tsakiya gaba daya.
An kashe shi ya na da shekaru 48 a duniya. Trump a jawabin sa ba gidan talbijin, ya bayyana Al-Baghdadi a matsayin kare, kuma ya fassara mutuwar sa da cewa “ya mutu kamar kare.”