Maidakin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi karin haske dangane da wata tirka-tirkar da ta faru tsakanin ta da iyalin Mamman Daura, a cikin Fadar Shugaban Kasa, Abuja.
A cikin wata tattaunawa da aka yi da ita a Sashen Hausa na Gidan Radiyon BBC, Aisha ta tabbatar da cewa ita ce a cikin bidiyon da aka nuno ta na hargowa saboda kulle ma ta kofar shiga gidan da aka yi.
Ta ce amma tsohon al’amari ne, ba kwanan nan ya faru ba.
Sannan kuma Aisha ta ce diyar Mamman Daura ce mai suna Fatima ta kulle kofar, kuma it ace ta rika daukar ta da bidiyon wayar ta ta na rikodin a gaban jami’an tsaron ta.
Aisha Buhari ta ce maigidan ta Buhari ne ya umarci iyalin Mamman Daura su fita daga gidan, aka ce su koma cikin wani wanda ma ya fi wannan girma.
An yi haka ne, saboda dan ta Yusuf ya dawo daga jiyyar raunin da ya yi sakamakon hadarin babur. Wato Buhari ya nemi Yusuf ya zauna a gidan da Mamman Daura ke ciki, domin samun saukin yadda zai rika samun kulawa daga mahaifiyar sa Aisha. Saboda gidan ba shi da nisa da cigan da iyalin Shugaban Kasa ke zaune.
“Na je domin na ga yanayin dakunan gidan, amma sai iyalin Mamman Daura suka hana ni shiga gidan, saboda sun kulle kofar. Daga nan sai na kewaya ta wata kofa a baya. Nan ma na same ta a kulle.” Inji Aisha.
A cikin wata hira da Fatima ta yi da Cable da kuma BBC Hausa, ita kuma Fatima ta yin karin haske kamar haka.
Ta ce: “Jami’an tsarona suna wurin amma sun kasa yin komai domin ‘yar gidan Mamman Daura – Fatima ce ta dauki bidiyon kuma har yau ni da su mun kasa yin komai kan lamarin.”
Haka zalika a hirar da aka yi a harshen Hausa ta nanata cewa Fatima ce ta dauki bidiyon, har tana yi ma ta dariya kuma ita ce ta rufe ma ta kofar dakin ajiyar kayayyaki.
A hirarta da BBC, Fatima ta bayyana cewa tun bayan hawan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shugaban ya bai wa mahaifinta (Mamman Daura) wurin zama a cikin fadar shugaban kasa wanda ake kira ”Glass House.”
Ta ce a lokacin da Yusuf Buhari ya samu hatsari a kwanakin baya, Shugaba Buhari ya bukaci Mamman Daura da ya koma wani gida da ake kira ”House No. 8”, wato gida mai lamba 8 domin a yi jinyar Yusuf a gidan da Mamman Daura da iyalan sa suke zaune domin wurin ya fi kusa da inda Aisha Buhari ta ke.
Fatima ta bayyana cewa ko da hakan ya faru iyayen ta ba su Najeriya, sai dai mahaifinta ya ba ta umarnin ita da ‘yar uwarta, cewa su kwashe kayansu daga gidan a ranar wata Asabar.
Ta bayyana cewa suna cikin kwashe kayan su ne sai ta ji hayaniya, domin ita tana can cikin kuryar daki ‘yar uwarta kuma tana dakin waje wanda ya fi kusa da kofar shiga gidan.
Ta ce kofar da ke waje an saka mukulli an rufe domin yawanci idan suna ciki su kan rufe ta.
Ta bayyana cewa ko da Aisha ta zo ta ga kofar a rufe, ”ta yi amfani da kujerar karfe wajen balle kofar.”
A cewar Fatima, wannan dalili ne ya sa ta dauko waya domin yin bidiyo don ya zama shaida.
An tambaye ta shin ko akwai wata matsala ne tsakanin su da ita Aisha Buhari. Sai Fatima ta ce babu wata matsala, domin dai kafin a hau mulki akwai zumunci mai karfi a tsakalin su. Amma abin ya sauya ne tun bayan da aka hau mulki, sai su ka fara ganin canji daga bangaren Aisha.
Ko da aka tambayi Fatima Mamman-Daura ko tun can dama ana samun rashin jituwa tsakanin Mamman-Daura da Aisha Buhari, ta bayyana cewa kafin Shugaba Buhari ya hau kan karagar mulki, suna zumunci lafiya kalau, amma tun bayan nan ne komai ya sauya aka fara samun matsaloli.
Discussion about this post