Yadda dan sanda ya rika danne wata ‘ya shekara tara son ran sa a dakin sa

0

A ranar Litini ne kotun dake sauraren kararrakin wadanda aka ci zarafin su dake Ikeja jihar Legas ta gurfanar da wani dan sanda Andy Eghonamien mai shekaru 40 da ake zargi da danne wata ‘yar shekara Tara kusan kullum.

Lauyan dake kare yarinyar Inumidun Solarin ya bayyana cewa dubun Eghonamien da aka fi sani da Boda Andy ko Ofisa ya cika ne wata rana bayan ya gama lalata da yarinyar a dakin sa.

A bayanin da ta yi a kotun yarinyar ta ce a wannan rana Boda Andy ya aike ta ne ta siyo masa madaran Naira 200, bayan ta dawo kuma sai ya lallabe ta a hankali har ya samu ta shiga dakinsa.

“ Boda Andy makwabcin mu ne dake zama a bayan gidan mu. Bayan na dawo daga makaranta a wannan rana sai ya aike ni in siyo masa madara. Da na dawo sai Boda Andy yace na shigo cikin dakinsa na ajiye madaran a kan tebur.

“Da na shiga dakin sai ya ce in zauna a kan gado kuma wai in cire wando na. Ina cire wa sai Boda Andy ya ciro azzakarinsa ya saka a gaba na. Yayin da yake haka sai na ji muryar yayata tana kira na.

“Boda Andy ya boye ni a karkashin gadonsa sai ya leko ya shaida wa yayata da ta nemi shiga dakin cewa bai ganni ba.

Yarinyar ta ce da ta koma gida sai ‘yar nata ta nemi dole sai ta fadi mata inda ta tafi tun bayan dawowarta daga makaranta. Daga nan sai yarinya ko ta fadi inda ta na.

” Daga nan sai yayata ta fadi wa iyayen mu duk abin da na fada mata. Iyaye na kuma ba su tsaya ko ina ba sai ofishin ‘yan sanda.

Yarinyar ta ce jami’an tsaro sun sa a kaita asibitin ‘Mirabel Center’ inda gwajin da likitoci suka yi ya nuna cewa an dade ana lalata da ita.

Lauyen dake kare Boda Andy, M.L Ezomo ya tambayi yarinyar dalilin kin fada wa iyayenta lokacin da Boda Andy ya fara lalata da ita sai yarinyar ta ce Boda Andy ya ce zai kashe ta idan ta fada.

“Boda Andy shi kadai ke lalata da ni sannan ya dade yana aikata haka da ni.”

Alkalin kotun Sybil Nwaka ya dage shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Oktoba.

Share.

game da Author