Shugaban Hukumar Gudanarwar Budaddiyar Jami’ar Najeriya (NOUN), ya bayyana cewa wasu tubbabbun ‘yan kungiyar Boko Haram sun yanke shawarar shiga jami’ar domin yin kwasa-kwasai na digiri.
Shugaban hukumar gudanarwar, wato Peter Okebukola ne ya bayyana wa manema labarai haka, a lokacin da ya ke jawabi wurin wani taron manema labarai da aka shirya hedikwatar jami’ar, a Gundumar Jabi, Abuja.
“Wasu rahotannin baya-bayan nan da mu ka samu daga wasu cibiyoyi ko rassan jami’ar sun nuna cewa wasu tsoffin tuban ‘yan Boko Haram su biyu sun yanke shawarar shiga NOUN domin samun digiri. Sun samu wannan damar ce da aka ba su ta yin karatun kyauta, tun daga digiri har digirgir, ba tare da sun biya ko sisi ba.
Haka kuma Okebukola ya kara da cewa ana ci gaba da samun karuwar masu shiga jami’ar daga daurarrun da ke gidajen kurkuku.
Da aka tambaye shi ko an dai yi kwakkwaran binciken tantance su, don gudun kada a dauki kara da kiyashi, sai Okebukola ya ce, “tuni NOUN ta yi wannan kwakkwaran binciken, an ma wuce wurin.”
Mata sun fi yawa a Jami’ar NOUN
Haka nan kuma NOUN ta ce yawan dalibai mata sun zarce maza, a Jami’ar NOUN, wato National Open University of Nigeria.
A jami’ar akwai kashi 53 bisa 100 duk mata, sai kuma kashi 47 bisa 100 ne maza masu karatu a jami’ar ta NOUN.
Sanarwar da NOUN ta fitar ta nuna cewa dalibai 110,006 su ka ci gaba da karatu a wannan zangon karatu na biyu na wannan shekarar.
Daga cikin su kuwa akwai maza 51, 467 sai mata 58,539.
Daga cikin su akwai dalibai 39,695 daga yankin Kudu maso Yamma, sai kuma 17,581 daga Kudu maso Kudu.
Daga Kudu Maso Gabas akwai dalibai 9, 328 sai kuma wasu 3,257 daga Arewa maso Gabas. Daga Arewa maso Yamma kuma akwai dalibai 7,116.
Daga Arewa ta Tsakiya banda Abuja akwai dalibai 13,141. A Babban Birnin Tarayya Abuja kuwa akwai dalibai 18, 991.