A yau Juma’a Babbar Kotun Tarayya ta bayar da belin Omoyele Sowore, a kan kudi naira milyan 100.
Kotu ta ce sai masu karbar beli biyu sun ajiye naira milyan 50 kowanen su, sannan za a karbi belin sa.
Sannan kuma za su kasance mazauna Abuja ne, kuma kada su fita daga Abuja. Haka nan kuma kotun ta ce idan Sowore ya samu kan sa, aka karbi belin sa, to kada ya kuskura ya shiga zugar wata zanga-zanga, ko wani taro mai kama da haka.
A yau ne dai lauyan sa Femi Falana ya kara neman kotu ta bada belin sa, tare da Mista Bakare da ake tuhumar su tare.
An kama Sowore mai jaridar SAHARA REPORTERS ne a bisa zargin cin yi wa kasa zagon-kasa, harkalla da kuma gada-gadar intanet.
Sowore wanda ya shafe kwanaki 60 a tsare ofishin DSS, ya yi takarar shugabancin kasa a zaben 2019.
Ya yi kokarin hada gangamin zanga-zanga mai suna #RevolutionNow, amma aka kama shi, kwana daya kafin a fito zanga-zangar cikin watan Agusta.
Discussion about this post