Taron tattauna hanyoyin inganta kiwon lafiya: Abubuwa hudu da za a fi maida hankali akai

0

Taron tattauna hanyoyin inganta kiwon lafiya wanda PREMIUM TIMES,PTCIJ,cibiyar PACFaH@Scale,gidauniyyar Pink Blue da kungiyar ‘Nigerian Governor’s Forum (NGHF) suka shirya zai tattauna matsalolin dake hana samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasarnan.

Za a fara wannan taro ne daga ranar Talata zuwa Laraba a Otel din ‘Nicon Luxury’ dake Abuja.

Wannan taro mai taken ‘Samar da kiwon lafiya na gari ga kowa da kowa: Mahimmiyar rawan da gwamnati da masu fada a jiki za su iya takawa domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.

A taron ma’aikatan kiwon lafiya,wakilan gwamnati, masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya da sauran mutane za su tattauna hanyoyin da suka fi dacewa domin ganin talakan Najeriya ya samu kiwon lafiya na gari sannan cikin saukin farashi.

Matakai da za a maida hankali

1. Warewa fannin kiwon lafiya isassun kudade yadda ya kamata

Rashin ware wa fannin kiwon lafiya isassun kudaden da ya kamata matsala ce da ta dade tana hana fannin samun ci gaba inda a dalilin haka ya haifar da munanan matsaloli a fannin.

Taron zai yi kokarin wayar wa mutane kai da kuma yin kira ga gwamnati game da matsalolin da fannin ke fama da su a dalilin rashin ware isassun kudade,rage wa fannin kason kudade a cikin kasafin kudin shekara-shekara da rashin samarda wadannan kudade akan lokaci.

2. Karkato da hankalin mutane kan neman sanin yadda ake kashe kudaden da gwamnati ke warewa fannin.

Rashin maida hankali da mutane basu yi game da yadda ake kashe kudaden da gwamnati ke ware wa fannin kiwon lafiya na ba wasu kalilan danan handane mafi yawa daga cikin kudade.

A dalilin wannan matsala ne ya sa cin hanci da rashawa ya samu gindin zama dirshan da a yanzu komai ya tabarbare.

Wannan taron zai wayar da kan mutane sanin yadda za su rika sanin abinda da ya shafi lafiyarsu a kasarnan

3. Mahimmancin samar da inshorar kiwon lafiya ga kowa

Tun bayan shekaru 12 da gwamnati ta kafa hukumar inshorar kiwon lafiya wato NHIS mutane kalillan ne a kasar nan ke amfana da shirin.

Sannan duk da haka kason dake amfana da shirin a haka ma na kukan cewa ba kowani ciwo bane shirin zai iya dauke maka maganin shi.

Taron zai tattauna batun yadda za a iya bunkasa shirin domin ci gaban mutanen kasa.

4. Rawan da sassan gwamnati za su iya takawa domin kawar da matsalolin da suma cukuikuye fannin kiwon lafiya

Wakilan gwamnati,ma’aikatan fannin kiwon lafiya,masu ruwa da tsaki da sauran mutane za su tattauna rawar da kowannen su zai iya takawa domin ci gaban fannin.

Share.

game da Author