TARON KIWON LAFIYA: Mahalarta sun yi tsokaci akan hanyoyin da za abi don farfado da kiwon lafiya a Najeriya

0

Taron tattauna hanyoyin inganta kiwon lafiya wandan PREMIUM TIMES, PTCIJ, cibiyar PACFaH@Scale, gidauniyyar Pink Blue da kungiyar ‘Nigerian Governor’s Forum (NGHF) suka shirya ya guda a yau Talata a babban birnin tarayya, Abuja.

An shirya wannan taro ne domin tattauna matsalolin dake hana samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Taken taron shine ‘Samar da kiwon lafiya na gari ga kowa da kowa: Mahimmiyar rawan da gwamnati da masu fada a jiki za su iya yi domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan’’ sannan ma’aikatan kiwon lafiya, wakilan gwamnati, masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya da sauran mutane za su tattauna hanyoyin da suka fi dacewa domin ganin talakan Najeriya ya samu kiwon lafiya na gari sannan cikin saukin farashi.

A jawabin maraba da Mawallafin jaridar ‘PREMIUM TIMES’ Dapo Olorunyomi ya bayyana cewa ginshikin kowacce al’umma ya dogara ne a bisa inganci da nasarorin da za a samu a fannin kiwon lafiya.

Ya ce dole sai gwamnatoci sun maida hankali matuka a wannan fanni kafin a iya cimma burin da aka sa a gaba. Sannan kuma ya yaba wa wannan gwamnati bisa kokari da maida hankali da ta yi matuka wajen ganin anyi nasara a harkar kiwon lafiya a Najeriya.

Jakadan kasar Japan a Najeriya Yukuta Kikuta ya yabawa kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi domin samar da kiwon lafiya na gari ga kowa da kowa a kasan a dalilin irin manufofin da gwamnagtin sa take kirkirowa domin nasarar haka.

Kikuta yace gwamnatin kasar Japan a shirye take data ci gaba da mara wa Najeriya baya domin ci gaban fannin kiwon lafiyar kasar.

Daga nan wakilin kungiyar gwamnonin Najeriya NGF Musa Ukaru kira yay ga gwamnatin tarayya da na jihohi, masu fada a ji da sauran mutane su hada kai domin inganta fannin kiwon lafiyar ganin cewa yawan mace-macen yara kanana da mata, cutar Kanjamau, zazzabin cizon sauro sun yi wa kasar katutu.

Ukaru ya kara da cewa NGF za ta maida hankali matuka wajen ganin tana taka mahimmiyar rawa domin inganta kiwon lafiyar kasar nan.

Bayan haka shugaban gidauniyar ‘ABC’ Chiedo Nwankwo ta bayyana cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta zauna domin tsara hanyoyin da suka fi dacewa domin kawar da matsalolin da fannin ke fama da su tare da daukan darussa daga kasashen da suka ci gaba.

A nashi jawabin tsohon shugaban hukumar inshorar kiwon lafiya ta kasa (NHIS) Muhammad Dogoya ya ce tabas Najeriya za ta iya cimma burin samar da ingantaccen kiwon lafiya ga kowa da kowa a kasar kafin nan da shekaran 2030 amma hakan zai yiwu ne kawai idan gwamnati ta maida hankali matuka wajen fifita fannin kiwon lafiyar a cikin manufofinta da ta saka a gaba.

Dogo yace kafa dokoki domin inganta fannin kiwon lafiya, zantar da wadannan dokoki, warewa fannin isassun kudade, hada hannu da sauran hukumomi domin inganta fannin, wayar da kan mutane sune za a fi maida hankali akai idan har ana so a cimma wannan doguwar tafiya dake gaba a kiwon lafiyar kasar nan.

” Dole sai sarakuna, malaman addini, shugabani masu kishin kasa da sauran mutane sun hada hannu wuri guda domin inganta fannin.

Shi ko Mai martaba sarkin jihar Gombe Abubakar Shehu III yayi tsokaci ne a akai akan irin mahimmiyar rawar da sarakuna za su iya takawa a cikin wannan tafiya da aka saka a gaba.

Sarki Shehu ya kara da yin kira ga sarakuna da masu fada aji a musamman Karkara da garuruwan mu da su rika taimaka wa gwamnati wajen wayar da kan mutanen su game da manufofin da a aka saka a gaba musamman wadanda suka shafi inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin rage yawan mace-macen mata da yara kanana, inganta yin allurar rigakafi, kawar da yunwa a yara da sauran su.

Za a ci gaba da wannan taro ranar Laraba.

Share.

game da Author