TARON KIWON LAFIYA: Hukumar NPHCDA ta roki gwamnati ta amince wa asibitoci su rika dauka da koran ma’aikata

0

A ranar Laraba ne daraktan fannin gudanar da bincike na hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa (NPHCDA) Garba Bulama ya yi kira ga gwamnati da ta bai wa asibitocin kasar nan damar iya dauka da koran ma’aikata cewa haka zai taimaka wajen inganta aiyukkan fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Bulama yace a mafi yawan lokutta asibitocin kasar nan na fama ne da rashin kwararrun ma’aikata wanda gwamnati ta dauke su aiki.

Ya ce a dalilin haka ya sa marasa lafiya ke fama da rashin samun ingantaccen kiwon lafiya a asibitocin gwamnatin dake kasar nan.

“Mafi yawan mutane kan koka da sakacin ma’aikatan kiwon lafiya a asibitocin gwamnati da aka gano cewa hakan na da nasaba a mafiyawan lokutta saboda rashin daukar kwararrun likitoci da ma’aikatan asibiti ne da ba a yi a kasar nan.

“ Samar wa asibitoci ‘yancin dauka da korar ma’aikata zai taimaka matuka wajen hana aukuwar matsalolin da asibitocin gwamnati ke fama da su kamar su rashin biyan albashi, rashin kwararrun ma’aikata da dai sauran su.

Bulama ya kuma yaba wa namijin kokarin da hukumar NPHCDA ke yi wajen ganin an samu nasara a ayyukan allurar rigakafi a kasar nan.

Ya ce sakamakon binciken cibiyar MICS da aka yi a shekarar 2016 zuwa 2017 ya nuna cewa allurar rigakafi ya karu daga kashi 33 bisa 100 zuwa 54 a Najeriya.

Wadannan duk suna a cikin jawabin da Bulama ya yi ranar Laraba a wajen taron tattauna hanyoyin inganta kiwon lafiya a Najeriya da ake yi a Otel din ‘Nicon Luxury’ dake Abuja.

PREMIUM TIMES, PTCIJ, cibiyar PACFaH@Scale, gidauniyyar Pink Blue da kungiyar ‘Nigerian Governor’s Forum (NGHF) suka hada wannan taro mai taken ‘Samar da kiwon lafiya na gari ga kowa da kowa: Mahimmiyar rawan da gwamnati da masu fada a ji za su iya takawa domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Matsalolin dake hana samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasar nan da samar da hanyoyin da suka fi dacewa domin ganin talakan Najeriya ya samu kiwon lafiya na gari sannan cikin farashi mai sauki na daga cikin batutuwan da ake tattauna a taron.

Share.

game da Author