Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta tabbatar da cewa tabbas ita ce aka nuno ta na fada a cikin Fadar Shugaban Kasa a cikin wani bidiyo.
Aisha ta amsa tare da tabbatar da sahihancin wannan bidiyo, a cikin wata tattaunawa da ta yi da manema labarai a filin jirgi na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Ta yi hirar ce tare da Dandazon ‘yan jaridu, kuma an yi ta watsa hirar a bidiyo, a yau Lahadi.
Aisha ta bayyana cewa ba wani abin mamaki ba ne don ta yi wata biyu ba a gan ta ba, ta na waje.
Ta bayyana cewa kimanin shekara 27 kenan a duk shekara idan an yi hutu, ta na tafiya wata kasa da ‘ya’yan ta domin su yi hutu, kuma su kasance tare da juna na wani dan tsawon lokaci.
Ta ce ko shekarar da ta gabata ma ta je hutun a kasar Spain, a lokacin da ‘yar ta Zahra ta haihu.
Daga nan ta gode wa ‘yan Najeriya bisa goyon baya da kuma addu’ar da su ke yi musu ita da Shugaba Muhammadu Buhari.
TABBAS NI CE NA YI HARGOWA A CIKIN BIDIYO
Aisha Buhari ta tabbatar wa masu yi mata tambayoyi da ke kewaye da ita, ciki har da wakilan NTA cewa wannan bidiyo da aka nuno ta na hargowa a cikin Villa, ita ce, ba sharri ba ne. Sai dai kuma ta ce amma bidiyon ba sabo ba ne.
“Idan kun lura ai yanzun nan na dawo kasar nan, wajen karfe 5 na asubahi. Saboda haka ba sabon bidiyo ba ne. Tsohon bidiyo ne na wani al’amarin da ya faru, amma ba sabo ba ne.”
A lokacin da ake ta yamadidin zargin auren da aka rika yada ji-ta-jitar za a daura tsakanin Shugaba Buhari Ministar Ayyukan Agaji da Inganta rayuwar al’umma, kwana daya kafin ranar Juma’ar da aka ce za a daura auren, an rika watsa wani faifan bidiyo, inda aka nuno Aisha Buhari ta na ta hayagaga da hargowa saboda an “rufe ma ta daki.”
An rika nuno ta, amma ba tare da nuno fuskar ta ba, ta na tambayar dalilin da ya sa aka rufe daki, alhalin akwai dimbin jami’an tsaro a cikin Fadar Shugaban Kasa.
An kuma rika jin ta na cewa me na yi muku? Sannan an ji wata muryar wata mata can a gefe ta na cewa, “ba mu san za ki dawo yanzu ba Gwaggo.”
BA NI DA TA CEWA A KAN ZARGIN AUREN BUHARI DA MINISTA SADIYA –Aisha Buhari
Yayin da BBC Hausa ta tambayi Aisha dangane da zafin auren da aka rika yayatawa, Uwargidan Shugaban Kasa ta ce ai dams ba tun yau aka fara baza ji-ta-ji-tar karairayi akan Buhari ba.
Da ta na magana a kan surutan auren, ta ce ita dai ba ta kasar, sannan kuma maganar wanda zai karyata ai ba ita bace, wadanda aka rika yin surutan a kan su, su ne ya kamata su fito sun karyata.
Aisha ta ce ita dai yanzu ai da auren ta, don haka babu ruwan ta. Amma kuma ta dan yi wani tsokaci cewa ita wadda ake surutun a kan ta, ba ta fito ta karyata ba, har sai da ranar daurin auren ta wuce tukunna.
Aisha Buhari ta dawo yau Lahadi bayan kwanaki 60 da ta shafe a London, inda ta ce baya ga hutun da suka je, ta kuma bi shawarar likitan ta, wanda ya ce ta kara zaunawa domin ta samu isasshen hutu a can.