A ranar Laraba ne wani daga cikin magabatan Aisha Bello da ta cinna wa kanta wuta a jihar Zamfara saboda saurayinta bai iya biyan sadakin ta ya bayyana rasuwarta ranar Laraba.
Aminu Mohammed ya fadi haka ne da yake hira da manema labarai a garin Gusau.
Mohammed ya ce Aisha ta rasu ranar Laraba da safe a babban asibitin Gusau a daidai likitoci suna kokarin canja mata bandejin da aka rufe kunan dake jikinta. Kwanakin Aisha 45 kwance a wannan asibiti.
“Tun daga wannan lokaci iyayen Aisha suke ta yin fadi ka tashi don neman kudin asibiti domin ceto ran ta.
“Mun kashe Naira 700,000 wajen nema wa Aisha lafiya ta hanyar gudunmuwa da ga mutane da abokan arziki, amma duk wadannan kudade sun kare akan Aisha. A jiya ma kafin ta rasu sai da aka nemi mu siya wasu magunguna na akalla Naira 26,000 amma kuma ma babu kudin.
Idan ba a manta ba a watan Satuban ne PREMIUM TIMES ta ruwaito labarin yadda Aisha ta cinna wa kanta wuta saboda saurayinta mai suna Umar bai iya biyan kudin sadakinta ba.
Aisha wacce ke da shekaru 17 na zama ne a Albarkawa, karamar hukumar Gusau.Sannan ta aikata wannan mummunar aiki ne saboda ta gaji da zaman kadaici.
Aminu Muhammed da abin ya faru a idon sa a wancan lokacin kuma mai unguwar kauyen Albarkawa ya shaida wa manema labarai cewa Allah yasa akwai mutane kusa da inda Aisha ta aikata wannan mummunar abu sai suka yi maza-maza suka kawo mata dauki suka kashe wutar kafin ta rasu a lokacin.
Muhammed ya ce wannan abin tashin hankali ya auku ne bayan iyayen Aisha sun bukaci saurayinta Umar ya biya kudin sadakin Naira 17,000, shi kuma Umar ya ce bashi da wannan kudi.
” Da Aisha na jin haka kuwa sai ta siyo galan din Fetur ta duldula wa kanta ta kyasta ashana. Sannan ko a daidai Aisha tana kokarin ta cinna wa kanta wuta kanwarta ta yi kokarin hana ta amma taki ji.