Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa sojojin Najeriya dangane da abin da ya kira irin namijin kokarin da suka yi wajen dakile ta’addanci da sauran tashe-tashen hankula a kasar nan.
Da ya ke jawabi a yau Talata ga al’ummar Najeriya, a Ranar ‘Yanci, Buhari ya jaddada cewa tsaro ya na da matukar muhimmanci, domin sai an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali sannan tattalin arziki zai inganta.
Don haka ya ce a kan wannan, sojojin Najeriya sun cancanci a yaba musu wajen kokarin da suka nuna suka dakile ta’addanci a kasar nan.
Buhari ya kara da cewa gwamnatin sa ta inganta bangaren sojoji ta hanyar sayo kayan fama da kuma inganta rayuwar su.
Daga nan kuma ya gode wa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya da kuma sauran kasashen da ake kawance da su, bisa gagarimar gudummawar da suka bayar wajen shawo kan ta’addanci a kasar nan.
Daga nan sai ya nuna irin ci gaban da aka samar da kuma wanda aka doshi samarwa a Ma’aikatar Harkokin ‘Yan Sanda.
Ya kuma bayyana irin rawar da sojoji suka taka wajen fatattakar ‘yan takifen yankin Neja Delta masu kai wa kamfanonin hakar danyen mai hare -hare.