Sojoji sun ragargaza sansanin ‘yan bindiga a Kaduna

0

Zaratan Sojojin Hadaka na ‘Operation Thunder Strike, Operation Whirl Punch da sojojin Atilare na 312, sun ragargaza sansanoni biyu na ‘yan bindiga a Jihar Kaduna.

Kakakin Yada Labarai na Bataliya ta 1, Ezindu Idimah ne ya bayyana haka.

Idimah ya ce an kai wa ‘yan bindigar wawan farmakai ne a jiya Lahadi tsakanin karfe 2 zuwa karfe 4 na yamma.

Ya ce wata majiyar mutane masu kishi ce suka sanar da tabbatar wa jami’an tsaron inda sansanonin su ke.

An yi raga-raga da wadannan sansanoni ne a Kankomi, kusa da Tantu da kuma kan Tsaunukan Goje, cikin Karamar Hukumar Chikun. Kamar yadda Idimah ya sanar.

“An banka wa sansanonin wuta, kuma an bindige dan bindiga daya, tare da samun bindiga AK47 daya, babura 3 da wayar hannu guda 2 tare da naira dubu 5,000 a wurin sa.”

Sau hudu kenan a cikin kwanaki 10 kacal sojoji na ragargaza sansanonin masu garkuwa da mutane a wurare daban-daban, a jihar Kaduna.

Hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da satar shanu ya yi kamari a jihar Kaduna da kuma sauran jihohin Katsina, Zamfara da Sokoto da Neja.

Ko cikin makon da ya gabata an ceto wasu dalibai shida da aka yi garkuwa da su daga kauyen Gwagwada. Kuma an kashe wasu masu garkuwa a hanyar Birnin Gwari daga Kaduna.

Tuni jama’a da dama suka kaurace wa bin titin Abuja zuwa Kaduna, suka koma hawan jirgin kasa, saboda tsoron yin kacibus da masu garkuwa da mutane, wadanda kullum kama su ake yi, kuma kashe su ake yi, amma sun ki karewa.

Share.

game da Author