Zaratan Sojojin ‘Operation Thunder Strike’ sun kubutar da dalibai shida na Makarantar Sakandaren Gwagwada, cikin Jihar Kaduna da aka yi garkuwa da su tun a farkon wannan mako.
Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojan Najeriya ta 1 da ke Kaduna, Ezindu Idimah ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Alhamis a Kaduna.
Kanar Idimah ya kara da cewa an kuma kubutar da wasu yara uku, tare da bindige masu garkuwa da mutane su hudu.
“Sojoji na cikin sintiri a yankin, sai suka samu labari daga majiya mai tushe cewa wasu masu garkuwa da suka addabi titin Abuja zuwa Kaduna, sun sato wasu dalibai wadanda ke kan hanyar su ta zuwa makaranta.
“Sojoji sun durfafe su, inda su ma suka bude wa sojoji wuta. Amma da suka ga lallai gaba da gaban ta, sai suka yi saranda a hannun sojojin kawai.
“Daya daga cikin masu garkuwar a nan take ya mutu, sauran uku kuma sun tsere, kowa ya kama gaban sa, amma da munanan raunukan harbi a jikin su.”
Ya ce daliban wadanda aka ceto daga hannun masu garkuwar, tuni sojoji suka damka su a hannun iyayen su.
An samu bindigogi da albarusai a hannun masu garkuwar.
A wani labarin kuma, a safiyar jiya Alhamis ne sojoji suka ratattaka wa mahara wuta a wani kwanton bauna da suka yi musu a dajin Soho Gaya, cikin Karamar Hukumar Chikun, Jihar Kaduna.
“An kashe mahara biyu, tare da samun bindiga guda daya.”
Discussion about this post