Sojoji sun damke kwamandojin Boko Haram 10, har da ‘Burgediya Janar’

0

Sojojin Najeriya sun bada sanarwar cafke wasu kwamandojin Boko Haram su 10, a dajin kauyen Bitta, cikin Karamar Hukumar Gwoza da ke Jihar Barno. An damke su a lokacin da su ke kokarin arcewa daga tsananin zabarin wutar da sojoji suka rika tirnika musu.

Kakakin yada babarai na sojojin bakin daga, Aminu Iliyasu ne bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar wa manema labarai a ranar Asabar, a Abuja.

Ya ce an damke su ne a ranar 9 Ga Oktoba, a lokacin da sojojin aikin musamman na Birgade ta 26 suka kai wani farmaki a kan su.

Iliyasu ya ce da yawan wadanda aka kama an gano cewa su ne suka tuka motocin yakin da suka kai wa garin Gwoza hari cikin 2014.

“Wadanda aka kama din sun hada da Shettima Mustapha Umar, Abba Buji, Alhaji Bukar Madu, wato KAHID, wanda shi mukamin sa a cikin kwamandojin Boko Haram, daidai ya ke da Burgediya Janar. Sai kuma Ali Hassan, wanda limamin Boko Haram ne, akwai kuma Alkali Laminu.

“Sauran sun hada da Bukur Mustapha, Buba Umaru (wai shi Black Uhuru) kuma ‘Burgediya Janar’ ne, wato KAHID, sai Madu Nosobe, Mustapha Hussaine da Umar Jeddum, dukkan su ‘yan cikin Karamar Hukumar Bama, a Jihar Barno.

Daga cikin wadanda sojojin suka kama, akwai Alhaji Bukar Modu, wanda suka ce sunan sa ne na 89 a jerin wasu rikakkun hatsabiban ‘yan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo.

Share.

game da Author