Shugabannin Afrika sun ce Goodluck Jonathan Gwarzon Dimokradiyya ne

0

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan cikakken gwarzon dan kishin dimokradiyya ne.

Issoufou tare da wasu shugabanni sun yi wa Jonathan wannan kyakkyawan yabo, jiya Laraba a wurin taron Tattauna Wa’adin Shugabanni a kan Mulki da ake gudanarwa a Yamai, jamhuriyar Nijar.

Ya ce ya kamata duk wani Shugaban Kasa da ke Afrika ta Yamma da ma Afrika baki daya, to ya yi koyi da Jonathan.

Shugaban na Nijar wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, ya ce yadda Jonathan ya amince ya sadakas ya fadi zabe kuma ya mika mulki lami lafiya, abin koyi ne ga shugabannin Afrika baki daya.

Ya kuma jinjina wa Nelson Mandela, saboda yin zango daya tal da ya yi. Shi ma tsohon shugaban Liberiya, Amos Sawyer ya jinjina wa Jonathan.

Da ya ke jawabi a wurin taron wanda tsoffin shugabannin Afrika ta Yamma da dama su ka halarta, Jonathan ya ce shata wa”adi kan masu mulki abu ne mai kyau domin kara wa dimokradiyya armashi.

Share.

game da Author