Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa ta kammala shiri tsaf domin yi wa mutane miliyan bakwai allurar rigakafin zazzabin shawara a jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Mannir Yakubu ya fadi haka a taron fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar ranar Litini.
Yakubu yace za a yi wa yara ‘yan watanni tara zuwa masu shekaru 44 allurar rigakafi ne a jihar ganin cewa cutar ya fi kama mutane masu shekaru irin haka.
Yakubu yayi kira ga magidanta, sarakunan gargajiyya, malaman addinai da dai sauran mutane da su hada hannu da gwamnati domin ganin an yi wa wadannan adadin yawan mutane rigakafin cutar.
Ya kuma yi kira ga shugabannin kananan hukumomin Danmusa da Kankara da su taimaka wajen ganin an yi nasara a aikin da aka sa a gaba.
Bayan haka shugaban Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Matakin Farko ta kasa (NPHCDA) Faisal Shuaib ya ce za a kwashi tsawon kwanaki 10 wajen yiwa mutane allurar rigakafin cutar a jihar.
Ya ce za a shiga kasuwanni, coci, masallatai, tashoshin motoci da sauran wurare domin yi wa mutane rigakafin cutar.
Idan ba a manta ba a watan Satumba ne Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Bauchi (BSHCDA) ta bayyana cewa akalla mutane 23 ne suka rasu a dalilin kamuwa da shawara a karamar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi.
Hukumar ta ce ta yi wa mutane 169 gwajin jini tun daga wancan lokaci zuwa yanzu. Mutane biyar ne aka samu cikin wadanda aka yi wa gwajin na dauke da cutar.
Discussion about this post