SHAWARA: EU ta tallafa wa jihohin Katsina da Bauchi miliyoyin naira

0

Tarayyar kasashen Turai (EU) ta agazawa jihohin Katsina da Bauchi tallafin Naira miliyan 31 domin dakile yaduwar zazzabin shawara a jihohin.

Idan ba a manta ba a watan Satumba be aka sanar da bullowar cutar a wadannan jihohi biyu da a kalla mutane 27 suka kamu da cutar sannan Wasu ma har sun rasu.

Bincike ya nuna cewa mutane sun kamu da wannan cuta ne bayan sun dawo daga ziyaran dajin Yankari dake jihar Bauchi.

Duk da dunbin magungunan allurar rigakafin cutar da kasar nan ke samu binciken ya nuna cewa jihohin kasar nan da babban birnin tarayya Abuja sun yi fama da cutar a wannan shekara na 2019.

Bayanai sun nuna cewa hakan ya samo asali ne a dalilin kin maida hankali wajen yi wa mutane allurar rigakafi akai-akai.

A dalilin haka EU ta bayyana cewa ta bada wannan kudade ga kungiyar bada agaji na ‘Red Cross International’ domin ganin an kashe su ta hanyoyin da ya kamata a wadannan jihohi.

Share.

game da Author