Satar Yaran Kano Da Akayi Cin Amanar Dokokin Zamantakewar Najeriya Ne, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Kasar Najeriya ta hadaka ce, kowa yana da ‘yancin yin addini daga cikin addinan da dokar kasa ta yadda dasu. Wannan shine tsarin da ake kai a Najeriya.

Don haka, cin amanar kundin tsarin mulki ne a samu wasu daga cikin al’umar kasar sun saci yaran wata kabila sun canza musu sunaye da addini. Har ma ana maganar siyar dasu.

Duk kabilar da take da kan-gado bazata goyi bayan haka ba, don abun ya zama yaqin sunquru, ko kuma nace dauki-dai-dai.

Mustapha Soron Dinki

Mustapha Soron Dinki

Abunda abokan zamanmu inyamirai suka yi mana shegantaka ce da cin amana don haka mun zirawa kotu ido muga mai zata yi tunda cin amana ne da zalunci.

Babban abun takaici shine, makomar rayuwar yaran, tunda Allah ne yasan cikin hayaniyar da suka shiga. Mutum 9 saikace raguna, sannan ga wadanda ba a san yawansu ba. Mun godewa Allah da ya tona assirinsu.

Sannan naji dadi da Kanawa suka zira ido su ga abun da mahukunta zasu yi, duk masanin shari’ah yasan wannan babban laifi ne.

Muna kira ga gwamnati, don ko dan uwanmu bahaushe ne ya saci ‘ya’yan wata kabila ya canza musu addini a kamashi a hukuntashi da gaggawa saboda a mayarwa da masu hakki hakkinsu. Ballantana kuma siyar dasu.

Wadannan bara-gurbin mutane daga cikin kabilar Ibo sun zalunci mutanen Kano da iyayen yaran da suka sata. Babbar matsala itace, yadda suka canzawa yaran siffa da addini saboda neman duniya.

Kanawa mutane ne masu bin doka, zamu jira muga hukuncin da hukuma zata yi saboda sun kafircewa dokokin zamantakewa.

Tunda nake ban taba jin haka ba a Najeriya, saikace lokacin cinikin bayi. To ko a kasar Libya da aka dinga siyar da ‘yan Najeriya a shekarun baya, saida duniya tayi Allah-wadai amma sai gashi wasu kawo kasuwancin Najeriya.

Gaskiya mu yanzu kanmu ya waye a Najeriya, bamu da lokacin zage-zage ma ballantana rikici da wata kabila. Mun barsu da dokar kasa ta hukuntasu.

Na jinjinawa jami’en tsaro matiqa don sun taka rawar gani a cikin shekaran nan wajen dakile ta’addanci iri-iri a fadin jihar Kano.

Haka akeso, aiki yafi surutu yawa, lallai mun godewa Allah, yaranmu sun dawo, kuma zamu cigaba da saka ido wajen tantance wadanda muke mu’amila dasu da sunan kasuwanci ko makwabtaka. Idan kuma ba haka ba, zamu samu kanmu a cikin dana-sani.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author