SARAR MACIJI: An horas da ma’aikatan kiwon lafiya 50 a jihar Bauchi

0

Cibiyar gudanar da bincike kan dafin cizon maciji dake jami’ar Bayero a jihar Kano (BUK) ta horas da ma’aikatan kiwon lafiya 50 kan hanyoyin kula da mutanen da maciji ya sara.

Wani likita a cibiyar Muhammad Hamza ya sanar da haka wa manema labarai a garin Bauchi ranar Laraba.

Hamza yace cibiyar ta horas da ma’aikatan hanyoyin gane ire-iren dafin maciji a jikin mutum da hanyoyin da suka fi dacewa wajen kula da mutum.

“ Mun horas da ma’aikatan kiwon lafiya dake aiki a manya-manyan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko dake jihar.

“Cibiyar ta yi haka ne domin karfafa guiwowin ma’aikatan kiwon lafiya kan aiyukkan kula da mutanen da maciji ya ciza.

Idan ba a manta ba a shekarar 2018 ne ma’aikatan kiwon lafiya ta yi kira ga mutane da su ci gaba da kula da kan su da yin hatara musamman a lokacin hunturu.

Ma’aikatar ta ce dafin maciji na iya sanya makanta,shanyewar bangaren jiki, yanke bangaren da maciji ya sara ko kuma mutuwa idan ba a gaggauta daukar mataki ba.

Rahotani sun nuna cewa mutanen jihohin Gombe da Filato basu da sukuni a dalilin yawa-yawan cizon maciji da ya addabe su.

Bisa ga rahotan mazauna karkara da manoma ne suka fi fama da wannan matsalar sannan rahotan ya kara nuna cewa kashi 8.7 ne kawai daga cikin su ke zuwa asibiti domin samun magani.

” A Mafi yawan lokutta idan maciji ya ciji mutum sai a nemi maganin gargajiya inda a dalilin haka mutane ke mutuwa saboda rashin ingancin da magungunan gargajiyar ke da su.

Bayan haka jami’in hukumar raba maganin dafin maciji na Najeriya Nandul Durfa ya bayyana cewa hukumar ta wadatu da kwalaben maganin saran maciji akalla 4000.

Durfa ya ce samun maganin da hukumar ta yi ya kawo karshen matsalar karancin sa da hukumar da asibitoci ke fama da shi.

Ya ce Najeriya za ta iya magance wannan matsala ne idan ta fara sarrafa wannan magani a kasar nan a maimakon siyowa da take yi daga kasashen wajen.

Hanyoyin da za su taimaka wajen hana macizai zama a muhalli da cikin gidaje

1. A daina barin tagogi da kofofi a bude ba tare da a na kula da duk wani motsi ba. Za a iya saka murfin kofa mai raga, kafin ainihin kofar shiga saboda kiyaye wa.

2. A tabbata an duba rassan itatuwa da kuma tarin ganye dake karkashin itatuwan da suke domin macizai za su iya zama a irin wadannan wurare.

3. Tattabata an tsaftace muhalli kamar su nome ciyawa da kawar da karikitan kaya domin hana samar da wurin kwanciya ga macizai.

4. Za a iya yin amfani da tafarnuwa domin hana macizai shiga cikin gida da zama a muhalli.

5. A tabbatar an kakkabe wurin kwanciya kafin a kwanta domin wasu macizan na iya boyewa a wurin kwaciyar mutum.

Abin da ya kamata a yi idan maciji ya sari mutum.

1. A gaggauta ba wanda maciji ya sara maganin kawar da ciwon jiki.

2. Kada a huda wurin da maciji yayi sara domin hakan na iya kawo zuban jini.

3. Kada a yawaita motsa wajen da maciji ya yi sara domin hakan na iya sa gubar macijin shiga wasu bangarorin jikin mutum.

4. A kwantar da wanda maciji ya sara ta gefe koda zai yi amai.

5. Kada a yi amfani ko kuma a sha maganin gargajiyya amma a gaggauta zuwa asibiti domin samun kulan da ya kamata.

Share.

game da Author