SAKACIN MA’AIKATAN ASIBITI: Malaman Asibiti na bukatar horo kan yadda ake tarerayar marasa lafiya

0

Idan ba a manta ba a makon jiya ne PREMIUM TIMES HAUSA ta bada rahoton yadda kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta koka game da irin yadda sakaci da nuna halin ko-in-kula na ma’aikatan kiwon lafiya ke nuna wa marasa lafiya ke neman ya durkusar da fannin kiwon lafiyar Najeriya.

PREMIUM TIMES HAUSA ta tattauna da wasu mazauna garin Abuja inda suka bayyana cewa lalle sakacin ma’aikatan kiwon lafiya na yin illa ga rayuwar mutane da kuma kawo koma baya a fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Sun lissafe wasu matsaloli da yayi wa fannin katutu, sun ki ci sun ki cinyewa.

1. Rashin daukan kwararan matakai wajen hukanta likitocin da suka aikata laifuka musamman irin haka.

2. Karancin ma’aikatan, wato likitoci da Nas nas.

3. Rashin tausayin marasa lafiya da likitoci ke nunawa.

4. Rashin aiwatar da kudirorin inganta fannin kiwon lafiya.

5. Rashin biyan ma’aikatan albashi mai tsoka.

6. Rashin horas da ma’aikatan kiwon lafiya da dai sauran su.

Wadanda aka zanta da su sun koka cewa baya ga matsalolin da ake fama dasu, akwai kuma rashin kwarewa da horo da wasu ma’aikata basu samu musamman wajen sanin yadda ake tarerayar mara sa lafiya.

Zainab Mohammed masaniyar magunguna dake aiki a asibitin Major Ibrahim dake Zariya, jihar Kaduna ta bayyana cewa rashin kafa dokar da zai hukunta ma’aikatan kiwon lafiya da basu san darajar aikin su ba da kuma rashin sanin hanyoyin da mutum zai bi don kwato hakkin sa idan aka wulakanta shi kokuma cin mutuncin sa a asibiti duk suna daga cikin matsalolin da ake fama da su.

Ita kuwa ma’aikaciyyar jinya a asibitin Gwamna Awan a Kaduna, Margaret Bonat ta ce ma’aikatan kiwon lafiya musamman likitoci da ma’aikatan jinya na iya kokarinsu wajen kula da marasa lafiya a asibiti.

Babban likitan asibitin Jikwoi Dakta Emeka Anene yace tabas fannin kiwon lafiyar kasar nan na fama da matsaloli da gwamnati ne kawai za su iya warware wadannan matsaloli.

Anene ya yi kira ga gwamnati da ta magance wadannan matsaloli da suke fama da su don zai taimaka wajen inganta fannin kiwon lafiyar Najeriya da kuma kara wa likitocin karfin guiwar yin aikin su.

Share.

game da Author