Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya goyi bayan rufe kan iyakokin da Najeriya ta yi, saboda bankin ya fahimci cewa matakan gyara ne aka dauka.
Zainab ta ce kasashen da ke makautaka da Najeriya su ne za a dora wa laifin dalilin rufe kan iyakokin.
Da ta ke magana da manema labarai a birnin Washington jiya Lahadi, Minista ta ce Najeriya ta rufe kan iyakokin ta ne domin ta sake karfafa dangantakar ta da wadannan kasashe da ke makautaka da ita.
“Shugaba Muhammadu Buhari bai so bada umarnin rufe kan iyakokin kasashen ba, saboda halin kuncin matsin tattalin arzikin da zai jefa wadannan kasashe.
A cewar ta an sha zama da aika sakonnin bukatar wadannan kasashe su rika kiyayewa da dokokin makautakar kasa da kasa, amma ba su kiyayewa. Maimakon abin ya ragu, sai ma kara muni ya rika yi.
“Tabbas rufe kan iyakoki zai shafi tattalin arzikin wadancan kasashe ma su makwautaka da mu.
“Kokarin da muka yi na rufe kan iyakar mu da makautan kasashe, mun yi ne domin a rika sauke kaya a tashoshin jiragen ruwan mu, wadanda ake karkatarwa ana saukewa a tashoshin jiragen ruwan wadancan kasashe.
“Wadannan kayayyaki da ake saukewa kamata ya yi a rika sauke su a kwantina a tashoshin ruwan Najeriya, kwastan su duba, su caje su haraji, su biya.
“Amma ba haka ake yi ba, sai su bari a can a bude kwantina, a rika kwasar kayayyakin kunshi-kunshi ana sumogal din su a Najeriya ta cikin barauniyar hanyar kan iyakokin mu.” Inji Zainab.
“Idan ba haka ba kuwa, to kananan masana’antun mu ne za su fi tagayyara sosai.”
Daga nan ta kara da cewa ana nan ana ci gaba da tattauna yadda Najeriya da sauran makautan kasashen za su rika kiyaye sharuddan cinikayya a tsakanin su.